’Yan fashin daji sun sako likitar nan da suka sace tare da da mijinta da ɗan ɗan uwansa a Jihar Kaduna, Dokta Ganiyat Poopola.
A ranar 27 ga watan Disamba 2013 ne aka yi garkuwa da su a gidansu da ke Kaduna, kafin daga bisani a sako mijin nata, Kamardeen Poopola wanda hafsan sojan ruwa ne a ranar 28 ga watan Maris, 2024.
Sai dai masu garkuwar sun ci gaba da riƙe yaron mai suna Abdulganiyyu tare da Dokta Ganiyat Poopola wadda likita ce a Asibitin Ido na Ƙasa da ke Kaduna.
Tsawon lokacin da ta shafi a tsare ya sa Kungiyar Likitoci Masu Neman Ƙwarewa ta Nijeriya (NARD) shiga yajin aiki domin matsa wa gwamnati lamba ta kuɓutar da ita.
- Tinubu ya naɗa muƙaddashin Babban Hafsan Sojin Ƙasa
- Ya kamata Najeriya ta daina biye wa Bankin Duniya da IMF — Jega
A ranar Laraba ’yan bindigar suka sako ta, kamar yadda shugaban kungiyar NARD, Tope Zenith Osundara tabbatar.