✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan shekaru 4 yana gwauranci, Dimeji Bankole zai auri diyar gwamnan Kebbi Bagudu

Dimije Bankole zai auri Aisha Shinkafi Sa’idu, diyar gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu.

An kammala shirin daura auren tsohon Kakakin Majalisar Wakilan Najeriya, Honarabul Dimeji Bankole da Aisha Shinkafi Sa’idu, diyar gwamnan Jihar Kebbi, Alhaji Atiku Bagudu.

Bankole wanda ya rabu da matarsa ta farko tun a shekarar 2017, ya shafe shekaru hudu yana rayuwar gwauraye inda aka rika yada jita-jitar yana hange-hange a ciki da wajen Najeriya wajen neman matar aure.

Auren da za a daura ranar Juma’a zai kawo karshen jita-jitar matar da ya samu shiga a wurinta tun bayan rabuwarsa da matarsa ta fari shekaru hudu da suka shude.

Amaryar da tsohon Kakakin Majalisar zai angwance da ita Lauya ce wacce ta yi karatu a Jami’ar Hull da ke Kasar Birtaniya kuma ta kasance jikanya ga mashahurin dan siyasar nan kuma tsohon Shugaban Kungiyar Tsaro ta Kasa, marigayi Marafan Sakkwato, Alhaji Umaru Shinkafi.

Uwar amaryar ita ce Hajiya Zainab Shinkafi Bagudu, daya daga cikin matan Gwamnan Kebbi, ta kuma kasance kanwa ga tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Alhaji Aliyu Shinkafi.

Wata sanarwa da dangin Bankole da ke Iporo a Jihar Ogun suka fitar ta bayyana cewa, makonni kadan da suka gabata ne aka kai karshen maganar kulla alakar auratayya tsakanin dangin biyu kamar yadda addinin Musulunci da kuma al’ada suka tanada.

Sanarwar ta ce Gwamnan Jihar Sakkwato kuma magajin Bankole a Shugabancin Majalisar ta Wakilai, Aminu Waziri Tambuwal shi ne ya jagoranci tawagar dangin angon zuwa gidan dangin amaryar domin neman auren ’yarsu.

Masu sanya idanun lura a kan al’amura na siyasa sun yi hasashen cewa auren da za a daura ranar Juma’a zai kara hada kan ’yan siyasar kasar nan duk da rarrabuwar kawunansu kasancewar Bagudu shi ne Shugaban Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar APC yayin da Tambuwal ya kasance Shugaban Kungiyar Gwamnonin jam’iyyar PDP na kasar.

Sai dai bisa la’akari da ka’idodin dakile yaduwar cutar Coronavirus, bangarorin biyu sun yanke shawarar gudanar da dan karamin shagali inda suke shawarartar dukkanin bakin da suka gayyata da su kiyaye dokokin da mahukuntan lafiya suka shar’anta.

Sun kuma roki sauran abokanan arziki da masu fatan alheri wadanda ba a aike wa katin gayyata ba a kan su fahimci uzurin da ya janyo faruwar hakan a wannan yanayi mai cike da rashin tabbas.

%d bloggers like this: