✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Bayan shekara 10, Buni ya soke haramcin hawa babur a Gabashin Yobe

Kwana hudu kafin zaben gwamna, Gwamnatin Yobe soke dokar haramta hawa babur mai kafa biyu da ta shekara 10 tana aiki a yankin Gabashin jihar.

Kwana hudu kafin zaben gwamna, Gwamnatin Yobe ta soke dokar haramta hawa babur mai kafa biyu a yankin Gabashin jihar.

Sama da shekaru 10 ke nan da Gwamnatin Yobe ta sa dokar haramta hawa babur mai kafa biyu a fadin jihar sakamakon rikicin Boko Haram.

Daga bisani gwamnatin ta janye dokar a yankunan Kudanci da Arewacin jihar sakamakon samun kwanciyar hankali.

Yanzu kuma Gwamna Mai Mala Buni ya dage haramcin hawan baburan a sauran yanki daya da ya rage na Gabashin Jihar (Zone A).

Kafin nan, a yayin da ake tsaka da yakin neman zaben gwamna da ’yan majalisar jiha, jam’iyyar adawa ta PDP a Jihar ta yi alkawarin soke dokar haramcin hawa babur idan ta ci zabe.

Hakan ya sa ake ganin Gwamna Mai Mala Buni ya shammaci PDP, ta hanyar dage dokar da take yakin neman zabe da shi.

Ko a makon jiya Aminiya ta kawo rahoton sassauta dokar takaita aikin baburan masu kafa uku, da ake kira Keke NAPEP a jihar.

Da yake sanar da dage dokar haramcin hawa babur a Gabashin Yobe, mashawarcin gwamnan kar harkokin tsaro, Birgediya Dahiru Abdulsalam (murabus) ya ce, Gwamna Buni ya dage haramcin ne daga ranar 6 ga Maris 2023 a kananan hukumomi bakwai na Zone A, wato: Bursari, Damaturu, Geidam, Gujba, Gulani, Tarmuwa da Yunusari.

Akwai sharudda:

An dage haramcin tare da sharudda kamar haka:

Baburan za su yi aiki tsakanin 6 na safe zuwa 6 na yamma kuma banda yin goyo ko yin sana’ar Achaba’ da bubur.

Duk mai babur a kananan hukumomin yankin sai ya yi rajista, lasisi da takardu daga Hukumar Kula da Tituna ta Jihar Yobe (YOROTA) da Hukumar Ba da Lasisin Motoci ta Jihar Yobe.

Kowane babaur zai yi aiki ne a cikin karamar hukumarsa kadai.

Duk mai babur da ya dauki fasinja za a sanya masa takunkumi.

Ba za a yi amfani da babur ba tsakanin wata karamar hukuma zuwa wata ba. Duk wanda saba za a saka masa takunkumi.

Don haka akwai buƙatar dukkan hukumomin tsaro da su sanya ido tare da tabbatar da bin waɗannan umarni da gwamnatin jihar ta shimfida.

%d bloggers like this: