✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan Sallah kuma sai me?

Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Wadannan kalmomi su suka kamata su fito daga bakin kowane musulmi da musulma da Allah Ya raya suka ga karshen watan Azumin…

Alhamdulillah! Alhamdulillah!! Alhamdulillah!!! Wadannan kalmomi su suka kamata su fito daga bakin kowane musulmi da musulma da Allah Ya raya suka ga karshen watan Azumin watan Ramadan na wannan shekarar ta 1434, bayan Hijrah ko mu ce na shekarar 2013, miladiya. Ba don kome ba godiya ta wajaba ga Allah ba, sai don irin arzikin da Ya yi mana mu da muka ga karshen watan lafiya, saboda ai an fara azumin da wasu, amma Allah a cikin ikonSa bai nuna masu karshen watan ba, bare a ce an yi Sallah  da su, kuma Ya yi haka ne ba don ba ya son su ba, mu kuma da Ya rayar da mu ba wai don Ya fi son mu bane, illah dai bisa ga ikonSa na yin dukkan abin da Ya keso, a kuma lokacin da  Ya so. Don haka mu da Ya rayar ya zama wajibi mu ce Allah mun gode. Don haka Allah mun gode.
Azumin watan na Ramadan na bana ya zo a cikin baiwe-baiwe da dama da Allah SWT Ya yi ga bayinSa, musamman mu na Arewacin kasr nan, wadanda da yardarm Alllah zan yi kokarin ganin na kawo wadanda hankali na ya iya bijirowa akansu. Da farko a cikin shekaru hudu da Arewa ta fada cikin gwagwarmayar `yan kungiyar Jam`atul Ahlis Sunnah Lid Da`awati Wal Jihad da aka fi sa ni da Boko Haram, wannan shi ne azumin watan Ramadan na farko da ita kanta Sallah karama da aka yi su cikin kwanciyar hankali, ba tare da an samu rahotannin kai hare-hare ba. Hatta Maiduguri babban birnin jihar Barno inda daga can gwagwarmayar `yan kungiyar Boko Haram din ta samo asali, a bana saboda irin zaman lafiyar da suka samu, har Hawan Daba mai alfarma Shehun Barno Alhaji Abubakar Garbai Ibn Ei-Kanemi, ya jagoranta a zaman shugulgulan Sallah, haka rahotanni daga sassa daban-daban na kasar nan ba, inda aka samu rahoton wani abin rashin jin dadi akan sukurkucewar matakan tsaron a lokacin shagulgulan Sallar, sai na hadurran ababen hawa da suke kokarin su gagari Kundila akan titunan kasar nan. Allah mun gode da wannan baiwa Ka kuma kara mana.
Tun kafin fara Azumuin waran na Ramadan, bisa ga al`ada al`ummar musulmi sukan yi tanadi kayayyakin abinci da abin sha da sutturu , wasu don kansu wasu kuma don kansu da sadaukarwa ko kyautarwa ga `yan uwa da sauran mabukata, wani abin sha`awa a bana ba inda aka samu rahoton tashin irin wadannan kayayyaki na masarufi, kamar su sukari da shinkafa da madara da man girki, har ma an fi kuka da tashin farashin kayayyakin da muke nomawa, irinsu gero da masara, wannan kuma kowa ya san dalili saboda tsululin damina da ake ciki. Akan yadudduka da sauran sutturu kuwa su ma nan sai hamdala. Allah mun gode da wannan baiwa taka, Ka kuma kara mana.
A bisa ga alheri da sadaka da kyauta da ciyarwa da wasu gwamnatocin jihohi da `yan siyasa da masu hannu da shuni kan daure su yi a cikin watan Azumin, nan ma sai godiya ga Allah. Don kuwa wasu gwamnatocin jihohi da `yan siyasa da wasu masu hannu da shuni, sun bayar da abincin buda baki da Zakkah, sun kuma tufatas. Wani abin sha`awa shi ne irin yadda kungiyoyin addinin Islama dama masu zaman kansu na cikin Ungunni da garuruwa da jiha suka kara kaimi wajen ganin sun tallafa wa Marayu da Zawarawa da kayayyakin abinci da sababbin sutturu, duk don alfarmar watan Azumin. Masu hannu da shuni da kungiyoyi sun kara matsawa gaba wajen ganin sun fanshi wasu daga cikin `yan gidajen Kurkuku, kamar yadda suka saba, ta hanyar biya masu tara, a wasu wuraren ma har sutturu aka tara aka kaima `yan gidajen Kurkukun, baya ga daye ko dafaffen abinci da wasu jama`a da kungiyoyi suka rika kaiwa `yan gidan Yarin. Allah mun  gode Ka kara mana kar Ka yi hushi da mu.
 Maluman addinin Islama sun bude karantarwar tafsirin Alkur`ani mai tsarki da Hadisai dana sauran littattafan ilmi da suka saba yi a Masallatai da Mjalisu daban-dabam ba dare ba rana, inda al`ummar musulmi kan je su saurara. Akwai kuma wadanda suka rinka daukar nauyin sanya irin wadancan karatuttuka a kafofin yada labarai, baya ga irin gudummuwar da masana suka rika bayarwa ta ilmantarwa a Jaridu da Mujallu, duk alfarmar watan na Ramadan.
 Mai karatu wasu daga cikin irin gagarumar gudummuwa da nasarorin da aka samu a cikin wancan watan mai alfarma na Ramada da ya gabata da hankali ya kai kansu, na kuma iya gabatar maka a wannan dan fili, a watan da kowa ke son ya yi alheri don neman dacewa da irin rahama da albarka da gafara da Allah Ya yi alkawarin zai yi wa bayinSa gari a cikinsa. Don haka addu`ata ita ce Allah Ya sa mun dace, akan alheran da aka gabatar kuma Allah Ya karfafi zukatan gwamnatocinmu da `yan siyasa da  masu hannu da shuni, kai har ma da talakawanmu da mu rika yawaita ayyukan alheri, bayan watan Azumin. Haka ba za ta samu ba har sai mun rika tuna darussan da muka koya a cikin watan na kamewa, ba wai daga ci da sha ba, a`a daga nisantar dukkan wasu abubuwan sabo kome kankantarsu, da kusanta dukkan ayyukan alheri da ganin muna aikatasu gwargwadon zarafi. Kar kuma mu manta da “Azumin sitti shawwal” Azumi shidda da ake a wannan watan na Shawwal.       
Maganar ganin wata dai an kasa warwareta, don kuwa ko a banan nan sai da aka samu sabanin ganin watan daga lokacin dauka zuwa lokacin ajiyewa, amma dai Alhamdulillah, ta ragu matuka. Al`ummar Musulmi Barka da Sallah. Allah Ya maimaitamana Ya sa ayyukan da muka gabatar a watan su zama karbabbu, amin summa amin.