An aike da karin jami’an tsaro zuwa yankin Sabon Gida da ke Jihar Zamfara, bayan an sace wasu dalibai ’yan mata biyu ranar Lahadin da ta gabata.
Wasu mahara da ake kyautata zaton ’yan bindiga ne dai suka sace ’yan matan su biyu, wadanda dalibai ne a Jami’ar Tarayya ta Gusau da ke Jihar, bayan sun balle gidan da suke haya a yankin na Sabon Gida.
- NAJERIYA A YAU: Yadda kalaman Abba Gida-gida ke yamutsa hazo a Kano
- Najeriya ta fara neman kai da danyen manta a kasuwar duniya
Maharan dai sun balle gidan ne ta karfin tsiya inda suka kulle masu gadinsa, suka kwace wayoyin daliban wadanda ke karatu a Sashen Nazarin Halittu na jami’ar, kafin daga bisani su yi awon gaba da su.
Sabon Gida dai nan ce unguwar da jami’ar take, kuma ba ta da nisa da mazaunin makarantar na dindindin. Galibi dai dalibai kan kama haya a can suna zama.
To sai dai bayan an kai harin, rahotanni sun ce daliban sun gudu sun bar gidajen nasu, amma daga bisani sun sake dawowa bayan an kai jami’an tsaro.
Har yanzu dai hukumar makarantar ba ta magantu ba a kan lamarin, yayin da duk yunkurin wakilinmu na jin ta bakin Kakakinta, ya ci tura.
Sai dai Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar ta Zamfara, SP Muhammad Shehu, ya ce tuni suka baza jami’ansu kuma suna can sun dukufa ganin sun ceto daliban cikin gaggawa.