Mai yiwuwa mai karatu lokacin da kake karanta wannan makalar labari ya game kasa da ma duniya baki daya cewa, Jam`iyyar APC, mai mulki da gwamnatin tsakiya a karkashin jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta kaddamar da `yan Majalisar zartarwar gwamnatin, kuma Ministoci kasa, bayan shiga wata na shidda da hawa kan karagar mulki ba tare da `yan Majalisar Zartarwar ba, kodayake dai ba wani sashi na Kundin tsarin mulkin kasar nan da ya tanadi wani yankakken wa`adi ga gwamnati walau ta jiha ko ta tarayya na lallai sai ta nada ministocinta ko Kwamishinoni. Sababbin ministocin 36, daya daga kowace jiha sun samu amincewar Majalisar Dattawa, bayan ha-maza-ha-matan da aka yi ta fama da ita a Majalisar, musamman tsakanin `yan jam`iyyar APC ya junansu da kuma `yan PDP mara sa rinjaye, kai ka ce daga karshe Majalisar ba za ta amince da sunayen wadanda aka rinka kada wa garwar kin amincewar akan su ba.
Mutane irin su Minista Rotimi Amaechi, tsohon Gwamnan Jihar Ribas da zai wakilci Jihar Ribas da Hajiya Amina Ibrahim, Wakiliyar Sakataren Majalisar dinkin Duniya akan shirin Muradan karni a kasar nan da za ta wakilci Jihar Gwambe da Hajiya A`isha Abubakar, tsohuwar ma`aikaciyar Bankin raya kasashen Afirka daga Jihar Sakkwato, su suka fi fuskantar mummunar adawa walau daga gwamnonin jihohinsu ko `yan Majalisar Dattawa na jihohinsu da sauran masu ruwa-da-tsaki na jam`iyyar APC da suka rinka zargin ba su ma san su ba cikin jam`iyyar ba. Hakan ya sa aka yi ta hasashen wadannan mutane uku ba za su kai bentansu gaban Majalisar Dattawan ba, amma daga karshe duk sun haye, ba wani kare bin damo.
Ya yin da aka kawo karshen dambarwar Hajiya Amina Ibrahim, aka tantance ta bayan samun tabbacin fadar shugaban kasa cewa jihar haihuwar ta, Jihar Gwambe take wakilta, shi Mista Amaechi kuwa `yan jam`iyyarsa ta APC da ke cikin Majalisar Dattawan suka yi iko da tanade-tanaden kundin tsarin mulki da hujjojin da ke gabansa na ba su da wata takamaimiyar shaidar shari`a a gabanta da ta tabbatar da Mista Amaechi ya yi wani laifi da har shari`ar ta yanke masa hukunci, kamar dai yadda shugaban masu rinjaye na Majalisar Sanata Mohammed Ali Ndume ya tabbatar, bayan tantancewar.
Da ma a baya a wannan fili lokacin da aka fara tantance rukunin farko na mutane 18, da wannan hayaniya ta neman ba za a amince da sunayen Mista Amaechi da Hajiya Amina Ibrahim ba na fadi cewa kowa zai haye, duk hayaniyar da ake yi, hayaniya ce da wakilan jama`ar suke yi don su kara rikita fahimtar inda aka dosa ga talakawan kasar nan, kuma batu ne na kowa ya san kowa, tsakanin `yan majalisar Dattawan da wadanda suka daure wa wadanda za a nada Ministocin gindi da su kansu wadanda za a nadan, don kuwa akasarin duk wanda aka kai sunan shi ya zama Minista a kasar nan tun tuni ba tun yau ba in ka bi diddiki za ka tarar da akwai inda ya daure akuyarsa gindin magarya, ba wai haka sakit, ko don cancanta ko tsantsar gaskiyarsa ta kai shi ba, illa sai don yana da uwa a gindin murhu.
Dadin-dadawa kamar yadda na fada a kwanan baya, tun da aka fara wannan dimokuradiyyar yau an shiga shekara ta 17, ba wanda Majalisar Dattawa ta taba kin amincewa da a nada shi Minista, ko shi Sanata Muslin Obanikoro daga Jihar Legas da a shekarar 2011, Majalisar Dattawa da farko ta ki tantance shi, saboda Sanatocin ACN uku daga jiharsa ta Legas sun ki mara masa baya, amma daga baya dai Majalisar ta amince da shi, don haka duk tsawon tarihin kasar nan mai `yancin kai a shekarar 1960, tarihi bai tabbatar da an ki amincewa da sunan wani ko wata da za a nada mukamin Minista don mutanen jiharsa sun ce ba sa tare da shi, a wannan karon kuma ba a kafa wannan tarihi ba.
Yanzu tunda an amince da wadanda za su zama Ministoci a wannan gwamnati da `yan kasa suka dade suna begen ganin kafuwarta a zaman za a samu CANJI daga irin mawuyaci halin kuncin rayuwa da mafi yawan `yan kasa suke ciki, musamman akan kyakykyawan zaton da ake ma Limanin CANJIN kuma Madugun gwamnatin, wato Shugaban kasa Buhari, to yanzu ba abin da `yan kasa suka zuba idanu su gani illa, irin CANJIN da sabuwar Majalisar Zartarwar za ta kawo, musamman yadda aka dade ba a fito da sunayen ministocin ba, ana ta laluben masu gaskiya da rikon amana za a nada. Mukamin Minisata a tarayya mukami ne mai nauyin gaske a tafiyar da gwamnatin, ta yadda akan dora nasara da rashin nasarar kowace gwamnati akan irin mutanen da ta nada Ministoci, kasancewar Minista wakilin shugaba na daya a ma`aikata. Don haka a tashin farko ya zama wajibi ya nemi cikakken hadin kan ma`aikatan da ya tarar a ma`aikatar, ta yadda za su rinka bullo da hikimomi da dabaru da basira da za su ciyar da dukkann ayyukan da ke ma`aikatarsa gaba don amfanin mutanen kasa. Kazalika ya rinka ba da gudummuwa mai ma`ana a cikin dukkan batutuwan da kudurorin da suka bayyana a tarurrukan Majalisar zartarwa na mako-mako.
Tunda yanzu an samar da Majalisar Zartarwar ta tarayyar da aka dade ana jiiira, ya kamata `yan Majalisar su fara aiki gadan-gadan, wajen ganin wannan gwamnati ta APC, ta bullo da cikakkun tsare-tsarenta, ta yadda za ta fuskanci matsalolin tattalin arzikin kasar nan kamar yadda ta dukufa wajen tabbatar da samar da zaman lafiya, musamman a shiyyar Arewa maso Gabas, inda `yan tada kayar baya suke cikin shekara ta shidda suna cin karensu ba babbaka, da kuma yadda ta dukufa da yaki da cin hanci da rashawa da kokarin kawo karshen sace-sacen shanu da sauran ayyukan ta`addanci. Samar da ajandar yadda gwamnati za ta fuskanci matsalolin farfado da tattalin arzikin kasar nan akan fannonin ilmi da ayyukan yi ga miliyoyin matasa da ayyukun noma da kiwo da hanyoyin kara tara kudin shiga, tun da dai yanzu gwamnatin ta dauki matakan yadda za su daina zurarewa da sauran makamantan ayyukan raya kasa da suka kamata a yi. Samar da wadannan manufofi su za su karfafa wa masu sa jari na ciki da wajen kasar nan da na sauran kasashen duniya da kugiyoyinsu da suka yi alkawarin tallafa mana, bayan shigowar wannan gwamnati, su shigo ko dai su zuba jarin ko kuma su kawo tallafin.
Daga karshe ina ga zai yi kyau matuka kuma zai kara kwarjinin gwamnatinsu, wadanda suka samu zama ministocin lallai su dage su kama wa Gwamnatin Muhammadu Buhari da jam`iyyarsu ta APC, cikin kamanta gasakiya da adalci wajen gudanar da ayyukansu. Duk abin da suka yi akasin haka, to, sun ci amanar shugaban kasa, sun ci amanar wadanda suka sa aka nada su, sun kuma ci amanar `yan kasa, sun kuma ci amanar kansu da kansu, sai kuma su saurari yadda Allah zai yi da su tun daga nan duniya. Ga `yan kasa masu fatan a fita daga kangin da ake ciki, akwai bukatar a ci gaba da addu`o`i ga shugabanni tun daga sama har kasa da kuma gaya musu gaskiya, su kuma shugabannin Allah Ya kara buda masu kirazansu su rinka karbar nasihar mabiya.