✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bayan kwana 20 da hawan Abba mulki muka so a rusa masarautun Kano — Ɗan Majalisa

Mun so a rushe duk masarautun Kano bayan kwanaki 20 da rantsar da Abba Kabir Yusuf.

Wani babban jami’i a Majalisar Dokokin Jihar Kano, ya ce wasu ‘yan majalisar sun so a rusa masarautun Kano kwanaki 20 bayan rantsar da gwamnatin Abba Kabir Yusuf.

Jami’in wanda ya zanta da wakilinmu ya ce babu abin da zai hana majalisar yi wa Dokar Masarautun Kano garambawul.

A wannan Larabar ƙudirin gyara Dokar Masarautun ya tsallake karatu na biyu bayan soma zaman yi wa dokar gyaran fuska.

Aminiya ta ruwaito cewa shugaban masu rinjaye kuma mamba mai wakiltar Ƙaramar Hukumar Dala, Lawan Hussaini Chediyar ’Yan Gurasa ne ya gabatar da ƙudirin.

Da yake tsokaci game da lamarin, ɗan majalisar ya ce, “Mun shirya tun da daɗewa kuma Allah ne kaɗai zai iya hana wannan gyaran.

“Mun so duk waɗannan sarakuna su tafi kwanaki 20 bayan an rantsar da wannan gwamnati amma ga mu a nan.

“Saboda haka gobe [Alhamis] za a yi zama na musamman a majalisar domin yin nazari tare da zartar da gyara.”

Sai dai shugaban marasa rinjaye na majalisar, Abdul Labaran Madari, ya shaida wa BBC cewa ’yan jam’iyyar APC 12 a majalisar ba sa adawa da gyaran matuƙar ba za a rusa ko ɗaya daga cikin masarautun biyar ba.

Haka kuma, Madari ya ce ba za su yi adawa da yi wa dokar gyaran fuska ba matuƙar ba za a tsige Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ba kuma ba za a maye gurbinsa da Sarki Muhammad Sanusi ba.

Ya ce duk da cewa ’yan majalisar na jam’iyyar NNPP suna da adadin da za su aiwatar da gyaran, sai dai hakan ba zai hana su adawa ba.

Madari ya ce yana zargin jam’iyya mai mulki ta kammala shirinta na rusa Masarautar Bichi tare da maido da tsohon Sarki Sanusi yayin da za a bai wa sauran masarautun hakimancin ƙananan hukumomi uku-uku kacal.

A watan Disambar 2019 ce gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta yi wa dokar masarautun jihar gyara, inda aka ƙirƙiro ƙarin masarautu gudu huɗu masu daraja ta ɗaya.

Masarautun sun haɗa da Gaya da Ƙaraye da Rano waɗanda aka ɗaga darajarsu zuwa masu daraja da ta ɗaya daidai da masarautar Kano.

Sai kuma Masarautar Bichi da aka ƙirƙiro, abin da ya sa Kano ta zama tana da masarautu biyar masu daraja ta ɗaya.

Masu adawa da matakin a lokacin sun soki ƙirƙiro sababbin masarautu a Kano domin a cewarsu hakan zai rusa tarihin masaratuar Kano na daruruwan shekaru, inda masarautar take da ƙima a idon duniya saboda faɗinta da kuma tasirinta.

Amma mutanen yankunan da aka ƙirƙiro wa masarautun sun yi maraba da matakin, suna cewa hakan zai ƙara kawo musu ci gaba da bunƙasa.

An dai jima wasu ɓangarori na kiraye-kirayen dawo da Sarkin Kano na 14, Muhammadu Sanusi II kan kujerarsa wanda gwamnatin da ta gabata ta tuɓewa rawani.