An girke karin jami’an ’yan sanda a yankunan da hare-haren ’yan bindiga suka yi kamari a Jihar Kebbi.
An yi hakan ne bayan ’yan bindiga sun kashe jami’an ’yan sanda tara, ciki har da Baturen Dan Sanda a wata musayar wuta a Karamar Hukumar Sakaba ta Jihar.
- ‘Jami’an gwamnati na wa jami’an tsaro manakisa a yaki da ta’addanci’
- Majalisa ta nemi Buhari ya ayyana dokar ta-baci a Najeriya
- Dan Majalisa ya raba wa al’ummar mazabarsa Naira miliyan 50 a Suleja
- Ronaldo ya gindaya sharadin rabuwa da Juventus
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi, DSP Nafiu Abubakar, ya shaida wa Aminiya wadanda aka tura din sun hada da Mataimakan Kwamishinan ’Yann Sanda guda uku.
Ya ce yin hakan ya zama dole domin a zakulo wadanda suka aikata laifin su girbi abin da suka shuka.
Aminiya ta gano cewa maharan sun kai harin ne domin satar shanu bayan ’yan bindigar sun kutsa kai daga jihohin Neja da Zamfara.
Bayan samun rahoto ne Baturen ’Yan Sandan da wasu jami’an ’yan sandan kwantar da tarzoma da ’yan banga suka kai dauki, inda aka kashe tara daga cikinsu a musayar wuta.