Jam’iyyar APC ta dauke aikin sayar da fom din takara na zaben 2023 zuwa Babbar Cibiyar Taro ta Kasa da Kasa (ICC) da ke Abuja.
Jam’iyyar ta dauke sayar da fom din takarar ne daga sakatariyarta ta Kasa, washegarin da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka sace tsabar kudi Dala dubu hamsin a wurin sayar da fom din.
- Kauyakun Giwa: Yadda ’yan bindiga ke sheke ayarsu a watan Ramadan
- Sallah: Yadda Mata Ke Shirin Kwalliyar Hijabi
Da yake sanar da sauya wurin sayar da fom din, Sakataren Yada Labaran Jam’iyyar APC na Kasa, Barista Felix Morka, ya ce an yi hakan ne domin saukake zirga-zirgar jama’a da ababen hawa, ganin yadda cincirindon jama’a ya haifar da cunkoso a kusa da sakatariyar jam’iyyar.
Felix Morka, ya kuma bayyana cewa Dala dubu hamsin din da aka sace mallakin wani mutum ne, ba na jam’iyyar ba.
“Ranar Laraba 27 ga Afrilu, 2022 wani mutum ya kawo rahoto cewa an sace mishi Dala 50,000 a kusa da babbar kofar shiga sakatariyar jam’iyyar.
“A sani cewa kudaden ba mallakin APC ba ne kuma ba su da alaka da sayar da fom din takara ko dauke sayar da fom din da aka yi daga sakatariyar jam’iyyar APC zuwa ICC.
“Kamar yadda aka riga aka tallata, kudaden sayen fom din takara ana biyan su ne a bunkunan da jam’iyya ta ayyana, kuma da Naira ake biyan su ba da Dala ba.
“Saboda haka, jama’a da ’yan jam’iyya su yi watsi da labaran kanzon kuregen da ake ta yadawa,” a cewar jam’iyyar.
Tun bayan da jam’iyyar ta fara sayar da fom din takara na zaben takara na 2023 ne dai masu son tsayawa takara suka yi wa wurin tsinke domin sayen fom.