Farfesan Ja-gaban zabi-sonka ya yi wa majalisar tsofaffin Haurobiya watsa-watsa, inda ya yi jawabi kan yadda za a sarrafa Katin-raddi, a daidai lokacin da Baudadden Joji ya bijiro wa jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge adawarsa da tsarin kada kuri’u, musamman ganin an toshe camama da cuwa-cuwa. Kuma wannan tsari zai kawo wa jam’iyyar cikas wajen murde kuri’un talakawan Haurobiya. Tuni dai Baudadden Joji ya sanar da duniya cewa, ‘da zarar Jam’iyya mai maganin radadi da zogin ciwon kurungu ta lashe zabi-sonka, babu abin da zai hana shi aron faden kolo, tun gari bai waye ba.
Akuyar-maman-daudu da ire-irensa sun bijiro da tambayoyi ga Farfesa Ja-gaban zabi-sonka, inda nan take ya ba su amsar Allah tsine uwar mai zuki-ta-malle. Yana gama batutuwansa, sai ya fice daga zauren Dauda-mai-maki da abokansa.
Hakika kulle-kullen makircin da jiga-jigan mai dan boto da sanda sjirge ke tsuwurwurtawa don su cakume Haurobiyawa. Domin musamman Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulkin mulaka’u ya dauko Fuffuken Fankan-fayau, ya bba shi mukamin bututun batutuwan mai dan boto, don kawai ya rika dura ashariya ga Shugaban Fafutikar Burin-huriyya, ya kirkira kiren zuki-ta-malle kama kare ka hada shi da zomo. Hakarsu dai ta gaza cimma na kwadi, don haka sai suka hada kai da Kanari Samun-bom-da-sauki, inda ya yi watsattsaken wasika ga Farfesa Ja-gaban zabi-sonka, ya firgita shi da cewa, ‘kasa ba tsaro, sai tsoro.’
Kanari ya rera baitukan wakokin son rai na jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, amma ba ta kai masa ba. Don haka sai aka lalubo Baudadden Joji don ya kulla wata kulalliyar. Kafin Dauda-mai-maki ya gayyaci Farfesa Ja-gaban zabi-sonka, sai da wakilan Mai dan boto da sanda jirge a karkashin jagorancinsa, suka gana da ’yan kamason zabi-sonka, wadanda suka nuna lallai wannan karon akwai tasgaro.
Baudadden Joji a kamo gafiya, muna nan muna jiran ganin ranar da za ka yi kabo da adabo. Dama Haurobiyawa su kosa da ganin an tunbuke turakun tafka ta’asa a kasa. Ka kuma gaggauta tun kasuwa bat a ci, ta waste ba, domin ka sayo faden kolo, ta yadda za ka kasance cikin shiri.
’Yan makaranta masu koyon watsattsake da buda wgagen littattafai a wannan farfajiya ta Dodorido, idan har ba ku kakafa wa kurungunku tagiyar Malam Mantau ba, za ku fasko cewa Ja-gaban ta-molar Mai dan boto da sanda jirge, wato Banga-banga Tukururu, shi ne ya yi harbatta mati da ta ingiza keyar Gwamna Mai kwarankwatsintsiya na birnin Dabo da Baba mai goro da Aman-cici da daukacin wadanda suka nuna adawarsu da takarar Shugaba Gudun-loko da Jona-tantin mulki. Bayan Messi mai masar ta-mola ya kora su, har sai da suka kulullube a giwar jam’iyya mai maganin zogi da radadin ciwon kurungu, sai aka bukaci ya roke su su dawo gida, amma suka ki.
Bayan Banga-banga Tukuru ya gama wasan ta-mola da mai dan boto, sai kuma aka ingiza keyarsa, inda aka lallashe shi ya karbi tarago da digar jirgin kasa, sai aka kawo Dumu-dumu Muzu-muzu, don ya sauya ’yan wasa, amma sai reshe ya juye da mujiya.
Tamkar dai yadda na bijiro muku da batutuwa a darasin makon da ya arce, Haurobiyawa sun gaji da mulkin mulaka’u na Mai dan boto da sanda jirge, shi ya sa sai neman maganin ciwon kurungu suke ta yi, musamman ganin yadda Shugaban Fafutikar Burin-huriyya ya tar cincirindon al’umma a Jihar Bararon-nono, inda mutanen su Alan-guburo suka yi masa maraba. Kai har ma ana yada cewa ya ziyarci garin ’yan matan Cibin-boko.
Watangaririyar da mai dan boto da sanda jirge ke yi, na tabbata bai rasa nasaba da watandar damin Hauro da Mace da zane da Santalla kwaiduwa suka tsuwurwurta a gabn na-mujiyar In-gwangwaje-in-wala. Kodayake shi ma Baudadden Joji ya dan taba tsakurar kasonsa daga lalitar tashar kwale-kwalen Haurobiya, inda ya hada karfi da Aminin Dabo, suka yi wa kasa wala-wala, hjar ta kai ga an jefa su a jarun. Jiga-jigan mai dan boto irin su Baudadden Joji suna da tarin yawa a kasar Haurobiya, don haka babu ta yadda za a yi Fuffuken-fankan-fayau ya wanke su, musamman ma jin cewa, Baba-ojo mai gonakin Ottawa, ya ce, wannan Man-kaza ne idan ka ba shi ‘tuwo da ’yan matsabbai,” sai kawai ya dauki bututun magana, ya yi maka rawa da waka. Shi kuwa Baban-gada-gada, tsohon Shugaba kasar Haurobiya da ke Jihar Ni-na-ja, cewa, ya yi ai tsohon mai jan linzamin kurkuridon tasi ne, Baba-ojo ya dauko shi, ya ba shi mukami, inda ya yi ta dura wa magabtansa buhun ashariya.
Haurobiyawa wadanda suka damalmala kasar Haurobiya a karkashin mulkin mulak’u irin na mai dan boto da sanda jirge, suna da tarin yawa, wasu mutanen boye ne, wasu kuwa koya ya gansu kiri da muzu. Kai a jerin wadannan miyagu har ma da wadanda ba su da wani matsayi da ya wuce na tsinannu, wato irin su Asarar-dan-kwabo da tsoho Kilaki da Kansakalin-kuku, wadanda ba su da wani aiki sai kulla wa Haurobiya kaidi, matukar suka hango za a taka musu burkin watandar dukiyar kasa.
Shi kuwa Malam Namando, abin da ya sanya na ki jero shi cikin wadanda suka yi katabus a mai dan boto, shi ne, shi muzurun Lami ne, kuma ai bai san bihim ba.
Ganin irin tabargazar da mai dan boto da sanda jirge ta tafka a kasar nan, ina ganin bai dace idan juam’iyya mai maganin ciwon kurungu ta kama ragama ta jefa su gidan jarun ba, kamata ya yi a tatse damin Hauron da suka yi kwashi-kwaraf dinsa, har suka jefa kasar nan cikin Haure-haure da hauragiya. Su kuwa tsofaffi irin su Banga-banga Tukururu da Baudadden Joji ko sun arce kada a cafko su, domin babu wata gudunmuwa ta ruguza kasa da za su sake tsuwurwurtawa. Fuffuken Fankan-fayau adabo! Mai dan boto dai ta shiga kofar hanci, ta balbalace.