✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Bauchi da Borno sun lashe gasar Musabaka ta kasa

A ranar Asabar da gabata ce aka kammala gasar  Musabakar Alkur’ani Mai girma karo na 32, inda wakilan jihohin Bauchi da Borno suka lashe gasar…

A ranar Asabar da gabata ce aka kammala gasar  Musabakar Alkur’ani Mai girma karo na 32, inda wakilan jihohin Bauchi da Borno suka lashe gasar ta bana.

Gasar, wacce Jami’ar Usman danfodiyo ke shiryawa duk shekara a matakin kasa, an gudanar da ita ce a Katsina fadar Jihar Katsina, inda aka shafe kwanaki bakwai ana fafatawa aiwata a tsakanin  mahaddata Alkur’ani da suka fito daga rukuni-rukuni a tsakanin ’yan takara maza da mata.

A wannan karo jihohi 32 ne suka halarci gasar, cikinsu har da Jihar Anambara. 

“Abu na farko dai da muka fara yi shi ne, tabbatar da cewa bakin da suka zo sun samu wurin kwana, ba wai ga masu gasar kadai ba, hatta  ’yan rakiyarsu da wadanda suka zo don kallo. Sannan sai maganar abinci da sauran wasu abubuwa na bukatuwar yau da kullum bakin gwargwado,” inji Mai Shari’a Musa danladi, daya daga cikin shugabannin shirya gasar.

Hafizin da ya zamo zakara a wannan gasa shi ne Amiru Yunusa, daga Jihar Bauchi. A bangaren mata kuma Amina Aliyu daga Jihar Borno ce gwarzuwar wannan shekara. Dukansu sun yi wa Allah godiya da  wannan nasara, sannan suka yi kira ga dalibai ’yan uwansu su kara bayar da himma a wajen neman ilimi.

Bayan kyautar motoci da suka samu gami da kujerun Makka, an kuma bi su da kyautar kudade da sauran kyaututtuka. Gwamnatin Jihar Katsina dai ta bayar da motoci 12 da Keke NAPEP 25 da Babura 25 da firij 10 da na’urorin kwamfuta Laptop domin rarrabawa ga wadanda suka yi nasara a matakai daban-daban na gasar.

Gwamnoni da sarakuna daga sassan Najeriya da Jamhuriyyar Nijar da manyan mutane da dama suka halarci rufe wannan gasa wadda aka yi ta a filin wasa na Muhammadu Dikko, wadda ta gudana cikin tsanaki da kuma matakan tsaro.