A kwanakin baya ne jaridu suka dauko rahotannin cewa an kammala gina makarantun tsangaya na zamani har guda 64, wadanda Gwamnatin Tarayya ta hannun Asusun Tallafa Wa Ilimi suka samar. Haka kuma, an gina wasu makarantun irinsu guda 25 kuma ana inganta su da kayan aiki. Dukkan makarantun nan, ana shirin mika su ga hukumomin jihohin da aka gina su kafin Disambar bana. A bara ma, Shugaban kasa da kansa ya jagoranci kaddamar da makarantun tsangaya guda 35 na farko da aka gina. Haka kuma Gwamnatin Tarayya da Bankin Musulunci (IDB) sun sanya hannu kan bashin dala biliyan 98 don bunkasa irin wannan ilimi a Maris, 2012 domin bayar da gudunmowa ta wannan fuska.
Duk da cewa irin wannan kokari na bunkasa harkar ilimin Almajirai abu ne da ya kamata a yi maraba da shi, to amma fa ya kamata mu lura cewa akwai matsaloli masu yawa a trattare da shi kuma ya dace mu natsu, mu nazarce su domin samo matita.
Idan muka lura, a halin yanzu akwai yara sama da miliyan goma (koma fin haka), kamar kuma yadda a kullum ake kara haiihuwar wasu, kuma ya zama dole a kula da harkar ilimantar da su. Abin da ba mu sani ba shi ne, irin wannan tsari na makarantaun tsangaya da kuma na zamani ko zai ci gaba da dorewa, ko kuwa akwai lokacin da za a hade su wuri daya a samar da tsari na bai-daya? A halin yanzu dai tsarin ilimi a Najeriya ya kasu kashi kusan uku – makarantun ’ya’yan attajirai, masu kai ’ya’yansu waje ko zababbun makarantun kudi a gida da kuma makarantun ya-ku-bayi da kuma makarantun tsangaya na almajirai.
A watan Mayu da ya gabata, Shugaban Majalisar Dattijai, Dabid Marka ya bijiro da wani kira ga gwamnonin Arewa su 19, inda ya yi kira a gare su da su yi kokarin haramta tsarin almajirci a Arewa, musamman saboda kamar yadda ya ce, almajiran sun zama wasu makamai na biyan bukatar karkatattun ’ya siyasa. Haka kuma, ya gano cewa tsarin na almajirici ba ya haifar da wani da mai ido, kamar kuma yadda ya gano cewa ashe tsarin ma ba ya da goyon bayan Musulunci, kamar yadda a baya ake tsammani.
“Almajirci, tsari ne marar tasiri, tsari ne da ke haifar da ’yan iska, don haka ba za mu bari ya ci gaba da gudana ba, domin ga mabiya wani addini na daban na shayin tsokaci game da batun, amma a yau na fahimta da cewa ashe ma tsarin ba na addinin Musulunci ba ne. Ina ganin cewa tuni ya kamata a ce an haramta shi. Don haka ina fata gwamnonin za su samu karfin halin haramta shi cikin kankanen lokaci.” Inji Shugaban Majalisar Dattijai.
Da Shugaban kasa da Shugaban Majalisar Dattijai, duk sun cancanci yabo, domin yadda suka nuna damuwarsu game da al’amarin almajirci da kuma yadda shi Babban Sanata ya sake tado da muhawarar. A can baya gwamnatoci da yawa sun yi kokarin yin wani abu game da batun amma suka kasa. Haka kuma, wasu shugabannin al’umma, kamar marigayi Janar Hassan Usman sun yi yinkurin bayar da shawrwarin magance matsalar. Gaskiya daya da ya kamata mu gaya wa juna, musamman ma shugabannin addinin Musulunci na Arewa da sauran masu fada a ji na yankin ita ce, mun dade muna yin shakulatin bangaro da batun nan na almajirci. Lokaci ya yi da ya kamata mu tunkari matsalar kai tsaye, kamar dai yadda marubuta irina a jaridar Daily Trust, Bala Muhammad da kaddam Sidk Isa suka bayyana a shafukansu na bukatar yin haka.
Bari mu sake jaddada bayanin manufarmu game da almajirci, domin kuwa a nan muna batun yadda ake tura yara ’yan shekara 4 zuwa 6 zuwa birane da nufin karatun Alkur’ani. A nan za ka ga suna zaune a zaure daya, babu sutrura, babu abinci sai dai yawon bara, sannan kuma suna cikin tsummokara da datti. Idan rashin lafiya ta kama su, babu wani magani. Iyayen da ke tura yaransu irin wannan tsarin karatu, suna bayyana cewa wai yaro ya fi samun karatu idan yana nesa da iyayensa. Amma ainahin gaskiyar ita ce, irin wadannan iyaye suna fakewa ne da guzuma suna harbi karsana. Ma’ana, suna jefar da hakkin da Allah Ya dora masu na kula da rayuwar ’ya’yansu. Haka za ka ga idan sun saki matansu ko kuma idan matan sun mutu, sai su tura ’ya’yan almajirci, su sake aure da ci gaba da hayayyafa. Yaran kuma su sake tura su almajirci wasu garuruwan.
Domin magance wannan al’amari, ya zama dole mu gaya wa juna gaskiya. A kwanakin baya na karanta mukalar da kaddam Sidk Isa ya rubuta game da al’amarin kuma ga abin da yake cewa: “Idan ana batun magance almajirci, ya kamata mu kalli al’amarin daga tushe, wato mu duba tanadin da shari’ar Musulunci ta ce game da batun, domin kuwa madamar ba a fahimtar da iyayen yara cewa bara ba ta da wani matsayi a Musulunci ba, to ba za su yi wani kokarin gyara al’amarin ba.
“Kamar yadda addini ya tanada, hakkin iyaye ne su ciyar, su tufatar, su ilimantar da ’ya’yansu sannan su koya masu tarbiyya da sana’a. Ba daidai ba ne su banzatar da su da sunan almajirci ba, da sunan haddace Alkur’ani. Allah ba zai taba tuhumar iyaye don yaronsu bai haddace Alkur’ani ba, amma zai tuhume su idan suka kasa tarbiyyantar da su, suka tura su cikin kunci da wahalar rayuwa ba tare da wata hujja ba.”
Wannan ita ce tsagwaron gaskiya, kuma dole ne mu amshe ta. Dole ne mu kula da hakkin da ke kanmu dangane da tarbiyyar yaranmu, kada mu banzatar da shi. Ba mu ne kadai matalauta ba a duniya, kula da tarbiyyar ’ya’yanku hakki ne da ya wajaba a kanmu kuma ba za mu ce mu damka wa wasu wannan aiki ba.
Batutuwan gaskiya game da almajirci a kasarmu
A kwanakin baya ne jaridu suka dauko rahotannin cewa an kammala gina makarantun tsangaya na zamani har guda 64, wadanda Gwamnatin Tarayya ta hannun Asusun…