A makon jiya ne aka samu labarin mata Musulmi da ke sansanin yi wa kasa hidima (NYSC) suka koka a kan yunkurin da mahukuntan shirin ke yi na neman hana su sanya hijabi a yayin da shirin ke gudana a duk fadin kasar nan. Daga nan ne kuma wadansu kungiyoyin kare hakkin Musulmi suka shiga ciki batun inda suka rika yin maganganun batunci ga shugabannin Hukumar ta NYSC a yunkurin neman hana matan sanya hijabi.
Shirin yi wa kasa hidima dai ya amince wa mata sanya gajeren hijabin da bai wuce gwiwa ba a tsawon makwanni biyun da za su kasance a sansanin horar da su. Kuma an dade da amincewa da yin haka.
Sai dai yadda shugaban shirin na NYSC Birgediya-Janar Johnson Olawumi ya kara jaddada wannan batu ne ta sa aka yi masa mummunan fahimta. Olawumi ya nanata cewa sanya dogon hijabi ga mata masu yi wa kasa hidima a tsawon kwanaki 14 da za su kasance a yayin horar da su, hukumar ba za ta amince da yin haka ba. Ya ce an dauki wannan mataki ne saboda halin tsaro. Ya ce mafi yawa daga cikin masu kai hare-hare da kuma tayar da bama-baman da ke yin sanadiyyar halaka bayin Allah babu gaira-babu-dalili suna amfani ne da dogayen hijabi wajen boye muggan makamai da bama-baman, don haka akwai bukatar a yi taka tsan-tsan don a kare dukiyoyi da kuma lafiyar al’umma. Wannan shi ne dalilin da ya sa hukumar ta jaddada soke yin amfani da dogayen hijabi a sansanin masu yi wa kasa hidima (NYSC). Ya yi wannan furuci ne a lokacin da ya karbi bakuncin kungiyar Matasan Musulmi Masu Yin Da’awah a ofishinsa da ke Abuja. Ya hori kungiyar ta wayar da kan membobinsu wajen amfani da kananan hijabi a tsawon makwanni biyun da za su kasance a sansanin yi wa kasa hidima (NYSC).
Sai dai a jawabinsa Shugaban kungiyar ta Matasan Musulmi masu yin da’awah Barista Lukman Hassan ya bayyana cewa sun kai wa Darakta-Janar din ziyarar ce don su nuna bacin ransu a kan yunkurin da ya yi na hana mata sanya hijabi a sansanin horar da su na NYSC. Ya bukaci mahukunta shirin su kyale kowane dan kasa ya gudanar da addininsa a sansanin ba tare da tsangwama ko nuna kyama ba.
A washagari ne kuma wata kungiya da ake kira Muslim Rights Concern (MURIC) ta shiga batun inda ta ce ba ta amince da batun hana sanya hijabi a sansanin NYSC ba. Daraktanta Farfesa Ishak Akintola ya ce Musulmi ba za su amince da batun hana su sanya hijabi a NYSC ba. “Ba mu amince da batun hana matanmu sanya hijabi a NYSC ba, yin haka tamkar cin fuska ne da nuna rashin hankali kuma wani yunkurin ne na neman hana mu ’yancin yin addini”.
A ra’ayinmu, bai kamata Darakta-Janar na NYSC ya fito fili ya fadi irin wadannan kalaman da za su iya tayar da fitina ba. Ba shi da ikon hana amfani da hijabin da mata Musulmi suke sanya wa a sansanin NYSC. Hasalima an dade ana amfani da hijabi don haka babu dalilin da zai nemi hana sanya hijabin a wannan lokaci. Haka su ma shugabannin kungiyoyin Musulmi masu yin da’awa da kuma masu kare hakkin Musulmi ba su kyauta ba da suka rika yin maganganu masu neman tayar da hankali a game da wannan batu.
Da farko dai tun cikin shekarar 1973 da aka kirkiro shirin yi wa kasa hidima (NYSC) matasa ke amfani da kayayyakin yin atisaye irin na jami’an tsaro da suka hada da wanduna da riguna da huluna da takalma masu rufe kwauri (boot) da sauransu a tsawon kwanakin da za su yi a sansanin don haka batun amfani da hijabi ma bai taso ba. Don haka batun da shugaban NYSC Birgediya Janar Johnson Olawumi ya yi a kan batun hijabi ma bai taso ba. Haka su ma maganganun da shugabannin kungiyoyin kare hakkin Musulmi suka yi a kan batun ba su dace ba. Duk da yake babu laifi idan kungiyoyin suka nemi hakkinsu, amma yakamata su rika yin taka tsan-tsan don ganin an kauce wa tayar da fitina a kasa musamman a wannan lokaci.
Kawo yanzu an samu fahimtar juna bayan kungiyoyin Musulmi da na mahukunta NYSC din suka sasanta a kan batun sanya hijabi. Da ma tun da farko ba a fahimci Darakta-Janar na NYSC din ba ne a kan batun sanya hijabi kamar yadda wata takarda da kungiyar Musulmi (MURIC) ta fitar. Ta ce shugaban ba yana nufin hana sanya hijabi ba ne kwata-kwata, amma mata za su rika amfani ne da kananan hijabi.
Muna fata nan gaba Hukumar NYSC da ma hukumomin gwamnati za su rika sanar da ’yan kasa muhimman bayanai don ganin an kauce wa rigingimun da ka iya tasowa. Haka kuma muna kira ga kungiyoyin kare hakkin addini da na dan Adam da su rika neman bayanai a kan abin da suka shige musu duhu kafin su dauki kowane irin mataki. Yin haka ne kawai zai kawar da shakku da kuma kawo zaman lafiya mai dorewa a cikin kasa da ma a duniya baki daya.
Batun hana sanya Hijabi a lokacin NYSC
A makon jiya ne aka samu labarin mata Musulmi da ke sansanin yi wa kasa hidima (NYSC) suka koka a kan yunkurin da mahukuntan shirin…