✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun burtali da wuraren kiwo a Najeriya

An dade ana samun sabani, kamar yadda ake samun fadace-fadace tsakanin manoma da Fulani makiyaya a sassa daban-daban na Najeriya. A mafi yawan lokaci, ana…

An dade ana samun sabani, kamar yadda ake samun fadace-fadace tsakanin manoma da Fulani makiyaya a sassa daban-daban na Najeriya. A mafi yawan lokaci, ana samun salwantar rayuka da ta dukiyoyi a sakamakon fadace-fadacen. Babban abin da ke haddasa wannan rashin jituwa tsakaninsu, ba zai rasa nasaba da kokarin makiyayan na neman wuraren kiwo ga dabbobinsu ba. A kokarinsu na sama wa makiyaya wuraren kiwo da burtaloli da nufin magance rashin jituwar da ke faruwa tsakaninsu da manoma, majalisu biyu na tarayya, wato Majalisar Wakilai da kuma Majalisar Dattijai, tuni suka fara kokarin samar dokokin da za su samar da damar kafa Hukumar Kula Da Burtaloli Da Wuraren Kiwo Ta kasa.
Akwai matsalolin da ake samu a kasar nan, wadanda suka hada da kwararowar hamada da fari da kuma dumamar yanayi, kuma ana alakanta matsalolin da yadda ake yawan sare dazuzzuka da kuma kwashe ciyayi domin ciyar da dabbobi da sauransu. Haka kuma, makiyaya kan wuce wuri, har su shiga wuraren da ba su dace ba, duk domin samar wa dabbobinsu abinci. Rashin jituwa da fadace-fadace kan faru tsakanin manoma da Fulani makiya, a sakamakon yadda wasu manoman kan babbake gonaki don noma, ta yadda ba a samar da burtaloli da wuraren kiwo.
A halin da ake ciki, kudurin dokar da Majalisar Wakilai ke aiki a kanta dangane da batun, har ta tsallake karatu na biyu. Kwamitin Al’amuran Noma na majalisar, tuni ya saurari ra’ayoyin jama’a dangane da wannan doka da suke kokarin samarwa. Idan har aka samu nasarar kafa Hukumar Kula Da Burtaloli Da Wuraren Kiwo Ta kasa, za ta yi kokarin samar da burtaloli da wuraren kiwo a dukkan sasssan jihohin kasar nan, wanda haka zai saukaka wa makiyaya samun hanyoyin bi da dabbobinsu da kuma wuraren kiwo.
Kamar yadda kudurin dokar ya bukata, hukumar za ta tuntubi dukkan gwamnonin kasar nan 36 da kuma Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, inda za ta nuna bukatarta ta na samar da burtaloli da wuraren kiwon dabbobi, daidai da dacewar doka. Bayan an samar da wuraren da burtalolin, hukumar kuma ta duba ta tantance su, za kuma ta nemi gwamnonin jihohin da su mika mata su a hannunta domin kiyaye su a matsayin burtaloli da wuraren kiwon dabbobi. Hukumar za ta yi haka ne tare da hadin-gwiwar kwamitocin hukumar na jihohi. Wadanda suke goyon bayan kudurin dokar da ma Sanatar da ta kirkire shi, wato Hajiya Zainab Kure da kuma Karimi Sunday Stebe na Majalisar Wakilai, duka sun bayyana tasirin da dokar za ta kawo idan an samar da ita. Sun bayyana cewa madamar aka samar da ita, za ta taimaka wajen magance ko kawo karshen rashin jituwa da fadace-fadacen da ake ta yawan samu tsakanin manoma da Fulani makiyaya a kasar nan. Su kuwa wadanda suke adawa da kudurin dokar a majalisun biyu na tarayya, sun nuna cewa, maimakon magance wannan matsala, idan aka kirkiro ta, za ta ma kara dagula al’amura ne, domin a cewarsu, akwai yiwuwar ma ta haifar da matsalar da ta fi ta baya muni, musamman ba zai magance matsalar da ke faruwa ba tsakanin ’yan kasa da baki ba. Wasu kuwa sun ma yi zargin cewa, wannan kudurin doka, ’yan siyasa daga cikin Hausawa ne da Fulani suka shigo da ita da nufin yi wa wasu kabilu wayon kwace musu gonaki da wurare mallakinsu.
A yayin da muke ganin wadannan cece-kuce da tsegumi da zarge-zarge a matsayin marasa tushe, duk da haka ba za a ce wannan kudurin doka bai da nasa kalubale ba, musamman ta fuskar tsarin mulkin kasa. Kamata ya yi daftarin kudurin dokar ya zama an tsara shi, ta yadda zai yi la’akari da muradin dokar da ke kasa, wadda ta tabbatar da kariya ga hakkin mallakar filaye da gonaki ga gwamnatin jihohi da kuma Babban Birnin Tarayya. Duk da cewa kudurin dokar ya sanya wannan ciki, amma su a ganinsu, abu ne mai sauki a roki gwamnatocin jihohi da Babban Birnin Tarayya, su mika filaye ga hukumar. Ita kanta hikimar kirkiro hukumar ta yi hannun riga da batun nan na rage matsalolin mulki a kasa. A lokacin da kwamitin da Stephen Orosanya game da yi wa tsarin gwamnati kwaskwarima ke neman a rage wasu hukumomi da cibiyoyin gwamnati, abu ne mai wahala a ce kuma za a nemi a sake kirkiro wata sabuwar hukuma daga baya. Abin da ya dace kuma ya kamata a yi shi ne, idan ma an ware filayen kiwon da burtaloli, to ya dace a ce suna karkashin kulawar hukumomin al’amuran noma da kiwo da ake da su jihohi. Idan an duba, tun lokacin Turawa, ai akwai burtaloli da filayen kiwo, don haka kamata ya yi a gano su, a farfado da su kawai, kowace jiha kuma ta kula da su, amma ba za a ce sai an kirkiro sabuwar hukuma ba.