✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batun Amusa, Makarantar Lauyoyi da hijabi

A ranar Laraba, 13 ga watan Disamba ne aka hana wata wadda ta kammala karatun zama kwararriyar lauya shiga dakin taron Internation Conference center da…

A ranar Laraba, 13 ga watan Disamba ne aka hana wata wadda ta kammala karatun zama kwararriyar lauya shiga dakin taron Internation Conference center da ke Abuja domin halartar bikin zama kwararriyar lauya. Farida Amusa, wadda ta kammala karatun digirin zama lauya a Jami’ar Ilorin, an hana ta shiga bikin ne saboda ta doge sai ta sanya hijabi. Lamarin ya janyo cece-kuce daga mutane da kungiyoyi da yawa a fadin kasar nan, wanda hakan ya nuna muhimmancin irin wannan lamarin.

Da yawa daga cikin kungiyoyin musulmi sun yi Allah wadai da wannan hukunci na makarantar ta zama kwararran lauya. Daga cikin kungiyoyin akwai Qungiyar ‘Yan Jarida Musulmi ta Najeriya (MMPN), Qungiyar Lauyoyin Najeriya (MULAN); Qungiyar Mata Musulmi (FOMWAN); Qungiyar Xalibai Musulmi ta Qasa MSSN, Majalisar Musulmin Abuja, AMF da Majalisar Tsofaffin Musulman Xaliban Jami’ar Obafemi Awolowo UNIFEMGA. Sauran sun hada da Majalisar Tattaunawar Musulmi, MCF; Qungiyar Musulmi ta yankin Kudu maso Yamma, MUSWEN da Majalisar Mutane Musulmi na Jihar Oyo, MUSCOY.

Shugaban Qungiyar ‘Yan Jarida Musulmi na Qasa (MMPN), Abdur-Rahman Balogun cewa ya yi, “Qin tabbatar da Farida Amusa ta zama kwararriyar lauya da makarantar zama kwararran lauya ta yi, an tauye mata hakkin addininta kamar yadda sashi na 38 na kundin tsarin mulki na shekarar 1999 kamar yadda aka gyara ya tanadar.” Balogun ya kara da cewa, “Mun yi amanna da cewa lauyoyi musulmi na Najeriya suma ya kamata a barsu su rika shiga kamar tawakrorinsu da ke sauran kasashen da suka ci gaba kamar yadda addininsu ya tanadar.”

Ita na Qungiyar Kula da Lamarin Musulmi [MURIC], ta yi kira ga Hukumar Kula Hakkin dan Adam [NHRC] da ta bincika yadda aka tauye hakkin addini a makarantar ta zama kwararran lauya, inda suka nanata cewa ya kamata a gyara tsarin gudanarwar makarantar. Shi ma shugaban Qungiyar Xalibai Musulmi, Jameel Muhammad ya kwatanta yadda aka hana amfani da hijabi a matsayin kin addinin musulunci. Inda ya ce, “Idan addini ya bukaci wani abu daga gare ni, babu wani taka dokar kasa da na yi. Ban ga dalilin da za a take min damar da Allah Ya bani, sannan kuma dokar kasa ta bani ba.”

Shugabar FOMWAN ta kasa, Halima Jibrin ta ce musulmin Najeriya za su tabbatar da cewa karatun Farida Amosa na lauya bai tafi a banza ba. Halima Jibrin, wadda ta gana da shugabancin MULAN tare da Farida ta tabbatar da cewa, “Rashin adalci da aka yi mutum daya kamar rashin adalci ne ga kowa.” Sannan ta bukaci lauyoyi da su dubi wannan lamarin da idon basira sannan su shawo kan lamarin ta yadda za su tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa za su samu kariya wajen gudanar da addinin da suka zaba daga wajen wadanda suke tunanin za su kare su.

Sarkin Musulmi, kuma shugaban Majalisar Qoli ta Addinin Musulunci [NSCIA], Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar ya nuna cewa bai ga wani abun magana ba a kan hijabi, inda ya ce hijabi na nufin shiga ta mutunci ga matan musulmi, wanda kuma yana cikin tsarin musulunci. Sarkin musulmin ya yi magana ne a Jihar Legas a wajen taro na kasa na cibiyoyin hulda da jama’a na musulmi (MPAC), ya ce yana mamakin yadda sanya hijabi zai zama wani babban abu da har macen da ta sanya hijabi za a rika tozartar da ita. Ya yi magana ne ta bakin wakilinsa a wajen taron, Wazirin Katsina Alhaji Sani Abubakar Lugga, inda ya kara da cewa sanya hijabi ba ai kawai shiga ta musulunci ba ce, har adinin Kirista ya amince da shi.

A daidai lokacin da Majlisar Wakilai ta kasa da umarci kwamitin ta na shara’a da kotunan tarayya ta bincika lamarin a makon da ya gabata, sannan ta kawo rahoto a cikin mako biyu, har yanzu babu sanarwa daga makarantar ta zama kwararran lauya. Yadda wasu daga cikin ‘yan kasa suka tayar da kashin wuya a kan wanan lamarin, ya sanya an canja yanashin shiga na bai daya na wasu makarantu da asibitoci domin a bar dalibai mata da ma’aikatan jinya su sanya hijabi. Duk da cewa ba ma kira ga dalibai su karya sanannaiyar doka, amma muna kira ga makarantar zama kwararren lauya ta gyara yanayin shiga domin ta bar lauyoyi mata su rika amfani da hijabinsu. Bari a sanya hijabin ba zai hana komai ba ga lauyoyin ko kuma koyon aikin zama lauyan.