✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Batanci: Mun yaba da hukuncin rataye Abduljabbar — Zauren hadin kan Malamai

Malaman sun ce kotun ta yi daidai da ta yanke masa da hukuncin rataya domin ya zama izina ga masu irin akidarsa

Zauren Hadin Kan Malaman Musulunci a Jihar Kano ta yaba hukuncin kisa ta hanyar rataya da Kotun Musulunci ta yanke wa Abduljabbar Nasiru Kabara kan batanci ga Manzon Allah (SAW).

A wata sanarwa da gamayyar majalisar malaman ta fitar, wadda Dokta Sa’idu Ahmad Dukawa ya sanya wa hannu, ta ce tun da aka fara shari’ar take bibiyar shari’ar kuma ta gamsu da hukuncin karshe da kotun ta yanke wa malamin.

“Wannan hukunci, muna fata, zai zama izina ga sauran masu irin wannan akida.

“Wannan majalisa na mika godiya ta musamman ga Alkali Ibrahim Sarki Yola, lauyan masu gabatar da kara da kuma dukkanin bangarorin da suka tabbatar da cewa an yi abin da ya dace wajen yanke hukuncin da ya dace ga wanda ake tuhuma”.

Ya kara da cewa an bai wa Abduljabbar duk wata dama da ta dace don ya kare kansa a kan dukkan tuhume-tuhumen da ake masa, amma ya kasa.

Aminiya ta ruwaito yadda Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke Kofar Kudu a birnin Kano ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.

Kotun ta yanke masa hukuncin ne bayan samun sa da laifi batanci ga Fiyayyen Hallita Annabi Muhammad (SAW).

Da yake yanke hukunci, alkalin ya umarci gwamnatin jihar da ta kwace masallatai biyu na Abduljabbar da kuma tarin litattafan da ya gabatar a matsayin hujja a gaban kotun.

Alkalin ya kuma haramta sanya hoton Abduljabbar, ko sanya karatuttukansa a dukkanin kafafen yada labarai.

Kotun ta bai wa malamin kwanaki 30 don daukaka kara kan hukuncin da ta yanke masa.