✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Batanci ga Sahabbai: An dakatar da malami daga yin wa’azi a Bauchi

Umarnin dakatarwar dai na kunshe ne a cikin wata wasika da ma’aikatar ta fitar dauke da sa hannun Kwamishinan ma’aikatar, Alhaji Ahmad Aliyu Jalam.

Gwamnatin jihar Bauchi ta bakin Ma’aikatar Harkokin Addini da Walwalar Jama’a ta Jihar, ta dakatar da wani malamin addinin Musulunci, Malam Abubakar Idris daga yin wa’azi a jihar.

An dai dakatar da malamin ne dake garin Azare a Karamar Hukumar Katagum ta jihar bisa zargin yunkurin tayar da zaune tsaye a cikin wa’azinsa ta hanyar yin batanci ga Sahabban Annabi (S.A.W).

Umarnin dakatarwar dai na kunshe ne a cikin wata wasika da ma’aikatar ta fitar ranar Laraba, 27 ga watan Afrilun 2021 dauke da sa hannun Kwamishinan ma’aikatar, Alhaji Ahmad Aliyu Jalam.

A cewar wasikar mai taken ‘Karya dokokin wa’azi da hudubobi na jihar Bauchi, “An jawo hankalin Gwamnatin Jihar Bauchi kan salon wa’azinka. Rahotanni sun nuna cewa kana cin mutunci da kuma yin batanci ga Sahabban Annabi (S.A.W) a cikin wa’azinka.”

Sai da Aminiya tra tuntubi malamin ta wayar tarho ya karyata zarge-zargen inda ya ce, “Maganar gaskiya babu kamshin gaskiya a cikin dukkan zargin da ake min. Kawai wasu mutane ne da muke da banbancin fahimta da su suke kokarin yin amfani da siyasa a cikin lamarin.

 “A zahirin gaskiya, gwamnati ba ma ta fahimci ainihin matsalar ba saboda babu wanda ya tuntube ni domin jin ta bakina a kan batun kafin daukar matakin. Kawai sun karbi korafi ne daga bangare daya sannan suka yanke hukunci.

“Bani da wani kokwanto ko tantama kan abubuwan da nake fade a cikin wa’azi na kuma bana tsoron kowa ya kaini gaban hukuma saboda na san babu wata doka ta Musulunci ko ta kasa da na karya,”inji Malam Abubakar.