✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Batanci ga Annabi: An kusa hallaka iyali 30

An yi zanga-zangar neman a hukunta matashin Sakamakon batanci ga Annabi (SAW) da ake zargin wani matashi mai suna Yahaya Sharif Aminu mazaunin Unguwar Sharifai…

  • An yi zanga-zangar neman a hukunta matashin

Sakamakon batanci ga Annabi (SAW) da ake zargin wani matashi mai suna Yahaya Sharif Aminu mazaunin Unguwar Sharifai Zangon Tudu a Karamar Hukumar Birni da Kewaye a Jihar Kano, yanzu haka iyayensa da ’yan uwansa sun shiga tsaka-mai- wuya da kasancewa cikin fargaba saboda yunkurin kone su da fusatattun matasa Musulmi suka yi niyyar  yi a ranar Lahadiin da ta gabata.

A ranar Asabar da ta gabata ce aka ce matashin wanda dan Faila ta Darikar Tijjaniya ne aka yi zargin ya fifita Sheikh Ibrahim Nyass sa kan Annabi (SAW) a  wata waka wacce ya sanya ta a shafin sada zumunta na zamani. Wakar da aka ce tsantsar cin mutunci ne ga Annabi SAW), kuma hakan ya janyo washegari Lahadi daruruwan matasa Musulmi suka yi wa  gidan su matashin tsinke, suka farfasa gidan tare da kokarin rushe shi da kone shi.

Binciken Aminiya ya gano cewa yanzu haka iyayen Yahya da shi kansa suna zaune a wasu wurare ne da ba a bayyana ba, bayan da jami’an tsaro suka kubutar da su.

Wani ganau, Malam Rabi’u Muhammad wanda aka fi sani da Murabba’i ya shaida wa Aminiya cewa, “Muna zaune sai muka ga mutane suna ta tururuwa zuwa kofar gidan su Yahaya, a nan kowa ya tsaya domin sanin abin da ke faruwa inda suka rika ihun cewa sun zo daukar matashin ne don haka ko ya fito ko kuma su kone gidan. In ban da Allah Ya sa jami’an tsaro sun zo a kan lokaci ba, to da Allah ne kadai Ya san abin da zai faru. An balle kofar gidan an farfasa gilasan tagogin gidan. Har shiga cikin gidan aka yi aka yi musu watsi da kaya. Allah dai Ya takaita lamarin.”

Malam Murabba’i ya bayyana matashin a matsayin wanda babu ruwansa da hayaniya, kuma ba ya shiga sabgar mutane. “To gaskiya shi ba mutum ba ne mai shiga cikin sabgar mutane ballantana har ka san ra’ayinsa a kan abin da ya shafi addini, ni dai na san ’yan gidansu har mahaifinsa ’yan Tijjaniya ne,” inji shi.

Wata matar aure da ke makwabtaka da gidan ta ce su kansu da suke makwabtaka da su sun shiga wani hali. “Wallahi ba karamin tashin hankali mu kanmu muka shiga ba, domin har katangar gidanmu sai da matasan suka sauke. Baya ga hana mu shiga da fita da aka yi,” inji ta.

Sai dai wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa ana zargin mahaifin matashin Sharif Aminu da zama daya daga cikin masu akidar Hakika. Majiyar ta yi zargin cewa wakar da matashin ya yi ta batancin, mahaifinsa ne ya rubuta masa ita, kasancewar shi mawakin yabo ne. “Dama ma mahaifin Yahaya an dade ana zarginsa kan bin tafarkin waccan akida ta Faira don haka da wanan abu ya faru ba a yi mamaki ba. Mutane ma suna cewa shi da kansa ya rubuta wa dan nasa wakar da yake shi mawaki ne. A yanzu haka a cikin gidansa akwai Zawiyarrsa da duk ranar Juma’a yake tara mutane masu bin akidarsu su yi wazifa daga nan kuma zuwa dare sai su yi ta wakokki irin nasu wanda mafi yawa wakokin yabon Sheikh Ibrahim Nyass ne,” inji majiyar

Rundunar ’Yan sandan Jihar Kano ta bakin Kakakinta DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce yanzu haka gidan yana karkashin kulawar rundunar don bayar da tsaro. “Bayan lamarin ya faru jami’anmu sun je wurin inda suka tarwatsa matasan da suka taru a kofar gidan tare da tserar da mutanenn gidan. A yanzu haka mutanen gidan suna karkashin kulawar ’yan sanda don ganin an ba su tsaro kamar yadda hakkinmu ne samar da tsaro ga rayuka da dukiyoyin al’umm,” inji shi.

An yi zanga-zangar la’antar matashin

A shekaranjiya Laraba wadansu mutane a karkashin jagorancin  wani mai suna Malam Alkassim Abdullahi sun gudanar da zanga-zangar lumana don neman hukuma ta dauki mataki a kan matashi Yahaya Sharif Aminu.

Daruruwan matasa sun gudanar da zanga-zangar a Hukumar Hisbah ta Jihar Kano inda suka samu tarba daga Kwamandan Hukumar Sheikh Sani Ibn Sina da wakilin Kwamishinan ’Yan sanda Alhaji Habu Sani da kuma DPO na Gwale da na cikin birni.

Musulmi a lokacin da suke zanga-zangar la’antar cin zarafin Annabi da matashin ya yi a Kano
Musulmi a lokacin da suke zanga-zangar la’antar cin zarafin Annabi da matashin ya yi a Kano

A cikin jawabin da ya gabatar, Malam Alkasim ya ce abin da matashin ya yi cin mutunci ne ga addinin Musulunci wanda ya kamata kowane Musulmi ya yi tir da shii.

Ya yi kira ga shugabannin da su gaggauta kamo matashin don ya fuskanci hukuncin laifin da ya aikata don ya zama izna gare shi da na baya.

A jawabansu, Kwamandan Hukumar Hisbah da wakilin Kwamishinan ’Yan sandan sun ba masu zanga-zangar tabbacin cewa za su yi duk mai yiyuwa wajen ganin wanda ake zargin ya zo hannu tare da gurfanar da shi gaban shari’a.

Haka kuma sun ja hankalin jama’a kan illar daukar doka a hannu inda suka neme su da bin matakin shari’a a duk lokacin da abubuwa makamancin wannan suka taso.

Ba wannan ba ne na farko

Al’amarin batacin ga Annabi (SAW) da ya faru a Kano a wannan mako ba shi ne karo na farko ba.

A wani lokaci cikin Watan Disamban shekarar 2015, wani mai suna Abdul Nyas ya aikata makamancin irin wannan batanci, wanda sakamakon haka Gwamnatin Kano ta gurfanar da shi a gaban kotu.

Gwamnatin ta fara gurfanar da Maryam Sayyada da wadansu mukarrabanta a gaban Kotun Lardi ta Shari’a da ke Rijiyar Lemo bayan da Abdul Nyas wanda ake zargi da aikata wannan danyen aiki ya gudu da ga Kano sakamakon hargitsin da kalamansa ga Annabi (SAW) suka jawo.

Daga bisani jami’an tsaro sun kama Abdul Nyas a Abuja kuma aka dawo da shi Kano domin fuskantar sharia’a. Bayan da aka dawo da shi Kano, an gurfanar da shi a gaban Kotun Lardi ta Shari’a da ke Rijiyar Lemo a birnin Kano inda aka yanke masa hukuncin kisa ta hanyar rataya.

Sai dai Abdul Nyas ya daukaka kara zuwa Babbar Kotun Kano (High court) domin kalubalantar hukuncin da Kotun Shari’ar ta aiwatar a kansa.

Amma lokacin da Alkalan Kotun biyu, Mai shari’a Yusuf Muhammad Ubale da Hadiza Sulaiman suka saurari karar, sun tabbatar da hukuncin da Kotun Shari’ar tayanke  wa Abdul Nyas  na kisa ta hanyar rataya.

Abdul Nyas ya sake daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara da ke  Kaduna. Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa har zuwa lokacin hada wannan rahoto, kotun ta Kaduna ba ta fara sauraron karar Abdul Nyas ba.

Kuma bincike ya nuna cewa, a yanzu haka Abdul Nyas na gidan kaso na Kurmawa yana jiran sauraron karar tasa a Kaduna. Ana samun matasa a baya-bayan nan da suke alakanta kansu da Faila -Tijjaniyya da suke wuce gona da iri wajen yabon marigayi Shehu Ibrahim Nyass, inda a karshe suke kaiwa ga cin zarafin Annabi (SAW).

Wannan ya sa wadansu daga cikin malaman Tijjaniya ’yan Failar suka fara barranta daga wadannan matasa.Wani faifan bidiyo ya nuna yadda hankalin daya daga cikin limaman Masallacin Kasa da ke Abuja, Farfesa Ibrahim Makari ya tashi har ya bayar da fatarwar a rika  kashe masu aikata haka.