Tsohon hadimin Shugaban Kasa Buhari kan Kafofin Sada Zumunta, Bashir Ahmed, ya sha kaye a zaben dan takarar dan majalisar wakilai na jam’iyyar APC.
Bashir wanda ke neman wakiltar kananan hukumomin Gaya da Ajingi da Albasu ya yi watsi da sakamkon zaben, saboda rikicin da ya ce ya barke a wurin zaben.
Dan Ganduje ya kai bantensa a zaben fidda gwani
“Ba a gudanar da zaben ba domin yawancin daliget ba a bar su sun yi zabe ba, ko kuma ba su damar shiga cikin dakin zaben ba;
“Wakilaina ba su sanya hannu kan wata takarda da ke nuna an yi zabe ba domin kuwa ba a bar su sun shiga wurin da aka gudar da zaben ba.
“Lokacin da na isa wurin a matsayina na mai takara ba a bar ni na shiga wajen kada kuri’a ba“, in ji Bashi Ahmed, kamar yadda BBC ta ruwaito.
An bayyana dan majalisar tarayya da ke ci a yanzu Abdullahi Mahmood Gaya a matsayin wanda ya lashe zaben.