Kasar Najeriya za ta fice daga kungiyoyin kasa da kasa 90 saboda kasa biyan kudin karo-karo na kungiyoyin.
Gwamnatin Najeriya ta dauki matakin a jiya yayin taron mako-mako na majalisar gwamnatin kasar wanda shugaba Buhari ya jagoranta.
Najeriya dai memba ce ta kungiyoyin kasa da kasa 310 inda kungiyoyin suke binta bashin da ya kai na Dala miliyan 120.
Ministar Kudi, Kemi Adeosun ita ta bayyana matakin da gwamnatin ta dauka ga manema labarai da ke fadar shugaban kasa.
Kemi Adeosun ta ce kasar za ta rage yawan kungiyoyin da take ciki da kashi uku don ta samu saukin biyan kudin karo-karon kungiyoyin.
Ta ce kasa biyan basussukan da ake bin kasar ya zama wani abin kunya ga kasar a idon duniya.