✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da warhaka Manyan Gobe (26)

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya taimaka, amin. A yau na kawo muku labarin Bala da Bello. Labarin na kunshe da yadda Bala…

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. Allah Ya taimaka, amin. A yau na kawo muku labarin Bala da Bello. Labarin na kunshe da yadda Bala ya yi asarar kyautar da mahaifinsa zai ba shi sakamakon son kai.
A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdulahi

Labarin Bala da Bello

Bala da Bello ’yan biyu ne. Bala na da son kansa sosai. Idan an ba su abu su raba sai ya debi mai yawa, sannan ya ba Bello kadan. Da yake abin duniya bai damu Bello ba, sai ya karba ba tare da ya ce wani abu ba.
Rannan mahaifinsu ya ce musu yana son ya raba dukiyarsa, amma yana son ya gwada su. Za su yi tafiya mai tsawo kafin rana ta fadi, kuma yanayin tsawon tafiya yanayin yawan dukiyar da za a ba kowane daga cikinsu.
Bello ya fara tafiya a hankali. Amma Bala ya fara gudu saboda yana son ya samu rabo mai yawa. Can sai ya gaji. Da yamma ta yi sai Bello sai ya dawo gida amma Bala bai dawo gida da wuri ba, domin kafafunsa sun yi zafi da kyar yake takawa.
Sai mahaifinsu ya ce Bello za a ba rabo mai tsoka domin ya dawo gida kafin faduwar rana. Abin ya yi wa Bala ciwo.
To, Manyan Gobe ina fata za ku so wa dan uwanku abin da kuke so wa kanku.