✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da warhaka Manyan Gobe 24

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon mun kawo muku Labarin Malami da dalibinsa. Labarin ya kunshi yadda Manyan gobe za su kasance…

Ina fata kuna cikin koshin lafiya. A wannan makon mun kawo muku Labarin Malami da dalibinsa. Labarin ya kunshi yadda Manyan gobe za su kasance masu bin kyakkyawan umarnin da aka ba su don su samu nasara a rayuwarsu.
A sha karatu lafiya.
Naku Bashir Musa Liman

Labarin Malami da dalibinsa

An yi wani dalibi da ke burin hawa doguwar igiya, musamman ma da shi aka zaba don ya wakilci makarantarsu a gasar hawan igiya.
“Hawa igiya akwai wahala, tana bukatar mayar da hankali. Tana da dadin kallo, sannan tana da wahalar koyo.” Malamin ya fada wa dalibinsa, a lokacin da yake koya masa hawan igiya.
“Idan ka yi amfani da wannan dogon karfen mai nauyi, to jama’a za su yi mamakin yadda ka dauki abu mai nauyi kuma kake hawan igiya, abin da ba su sani ba shi ne, wannan karfen zai rika taimaka maka ne.” Ya sake cewa da dalibinsa bayan ya kalli karfen.
dalibin ya dauki karfen sannan ya fara hawa igiyar, ai nan da nan ya kware wajen hawa igiya.
Wata rana sai dalibin ya fada wa malaminsa: “Ina ganin zan fi samun sauki da kuma sakewa idan har ban dauki karfe mai nauyi ba, saboda babu wani abu da  zai dame ni.”
Malamin ya ce masa a’a, karfen na taimaka masa ne wajen daidaituwa a kan igiyar ne. dalibin ya yi watsi da abin da malaminsa ya fada masa, wato ya jefar da dogon karfen, sannan ya fara hawa igiyar, hankalin malamin ya tashi a lokacin da ya ga dalibinsa ya fara hawa igiyar babu dogon karfe, kamar zai tsawatar masa sai ya kyale shi, don ya nuna masa kuskurensa. Bai je ko’ina ba ya fado, ya ji ciwo a hannunsa, sannan ya samu targade a kafarsa ta dama.
“Ka ga abin da nake fada maka ke nan, duk wanda bai bi kyakkyawan umarnin da aka yi masa ba, to zai yi kuka da kuma da-na-sani.”
dalibin ya roki malaminsa afuwa, sannan ya yi alkawarin ba zai sake bijire wa umarninsa ba.