✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da warhaka Manyan Gobe 21

Ina fata Manyan Gobe na cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku labarin Zaki da Namun Daji. Labarin yana dauke da darasin kowace…

Ina fata Manyan Gobe na cikin koshin lafiya. A wannan makon na kawo muku labarin Zaki da Namun Daji. Labarin yana dauke da darasin kowace halitta tana da gudunmuwar da za ta bayar a rayuwa. Ina fata za ku bi labarin don cin ribar darussan da yake koyarwa.
A sha karatu lafiya

Labarin Zaki da Namun Daji

Wata rana yaki ya tunkaro namun daji, sai zaki ya kira sauran namun daji don su tattauna yadda za a tunkari abokan gaba. Bayan sun hallara sai ya ce giwa ce za ta dauki kayan yaki saboda karfin da take da shi.
Bayan ya kalli bauna sai ya ce mata ita za ta rika amfani da kahonta wajen tsorata abokan gaba. Daga na ya kalli dila ya ce za ta rika tsara dabarun yaki. ta gyada kai, hakan ya sanya ya tafiyar da kallonsa zuwa ga sauran namun daji, sai dai kafin ya ce wani abu, sai kura ta ce idan haka ne mene ne amfanin gayyato zomo da jakin dawa kasancewar ba su da karfin fafatawa a wurin yaki.
“Babu wanda ba shi da rawar takawa, sai mun hada hannu gaba dayanmu kafin mu samu nasara. Jakin dawa zai sama mai busa mana kugen yaki, hakan zai karfafa mana zuciya har mu samu nasara a kan abokan gaba. Zomo kuma saboda gudunsa zai kai labarin samun nasararmu a kan abokan gaba zuwa gida, don hankalin wadanda suke gida ya kwanta.” Inji Zaki.
Sauran namun daji suka gyada kai domin sun gamsu kowane a cikinsu yana da gudunmuwar da zai bayar don a samu nasara.

Sanarwa
Manyan Gobe za ku iya turo da hotunanku zuwa wadannan adireshin imel: [email protected] ko [email protected]
Ku rika sanya cikakken sunanku kafin ku turo da hotunan.