✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da warhaka Manyan Gobe 17

Yaya azumi? Ina fata kuna azumi, ba wai na tsoma gaya a miya kuke yi ba. A yau na kawo muku labarin makaho mai fitila.…

Yaya azumi? Ina fata kuna azumi, ba wai na tsoma gaya a miya kuke yi ba. A yau na kawo muku labarin makaho mai fitila. Labarin ya kunshi illar mutum ya rika sa ido a kan abin da bai shafe shi ba. A sha karatu lafiya.
Taku: Amina Abdullahi

Labarin Makaho mai fitila

An yi wani makaho a wani kauye da mutane ke fama da matsalar wutar lantarki. A kauyen idan dare ya yi mutane kan kunna fitilarsu su rika hira kafin su kwanta.
Wannan makahon yana da hazaka wajen wanke fitilarsa kowane yammaci, da zarar gari ya yi duhu sai ya kunna ta. Ko da unguwa zai je sai a gan shi rike da fitila. Wannan al’amarin yana ba mutanen kauyen mamaki sosai.
Wata rana da daddare ya fito daga gidansa rike da fitla kamar yadda ya saba, sai ya hadu da wasu mutane suna wucewa a kan hanya, daga nan suka rika tsokanarsa: “Haba malam makaho in ban da rigimarka mene ne amfanin rike fitila, dare da rana duk daya ne a wurinka. Kowa a kauyen nan ya san kai makaho ne, amma ka rika yawo da fitila?”
Sai makaho ya ce musu “Ina rike wannan fitilar ne don masu idanu, domin idan babu fitila ba za ku iya gani na ba, hakan zai sa ku yi mini lahani. Amma idan kun gan ni rike da fitila za ku iya taimaka mini, ko kuwa ku kauce idan na zo wucewa.” Sai abin ya ba su tausayi, sannan kunya ta kama su, har suka ba shi hakuri.