✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da warhaka Manyan 3

Da fatan kuna mayar da hankali a kan karatu. A yau na kawo muku labarin hankaka da tulu. Labarin ya kunshi yadda Manyan Gobe za…

Da fatan kuna mayar da hankali a kan karatu. A yau na kawo muku labarin hankaka da tulu. Labarin ya kunshi yadda Manyan Gobe za su sami mafita idan sun kasance masu kokari da kwazo.
Taku: Gwaggo Amina Abdullahi

Labarin hankaka da tulu

Akwai wata macen hankaka da kishin ruwa ya dame ta. Can sai ta hango ruwa a wani tulu. Bayan ta sauko ne sai ta tabbatar ruwan ta hango. Sai ta yi kokarin sanya kanta a cikin tulun domin ta sha ruwan, amma kan nata ya gagara shiga cikin tulun.
Can sai wata dabara ta fado mata. Ta samu duwatsu ta rika jefawa a cikin tulun. Sai taga yawan duwatsun na kara dago ruwan. Haka ta rika yi har ruwan ya iso bakin tulun. Sai ta sanya bakinta ta sha ta koshi.
Da fatan Manyan Gobe za su dauki darasi daga wannan labarin. Kun ga, kokarin macen hankaka da dagewarta ne ya sanya ta samu ruwa ta sha ba don haka ba da kishi ya kashe ta.