✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka da Sallah!

A ranar Talatar da ta gabata ne aka gudanar da Sallar Layya wadda aka fi kira da Babbar Sallah. Kamar yadda aka saba ne a…

A ranar Talatar da ta gabata ne aka gudanar da Sallar Layya wadda aka fi kira da Babbar Sallah. Kamar yadda aka saba ne a Litinin da ta gabata ne aka yi hawan Arfa.
A lokacin wannan sallar ne ake yin layya wato yanka dabba don sadaukarwa ga Allah SWT. An fara layya a lokacin annabi Ibrahim (AS). Daga nan aka ci gaba da yinta a duk ranar 10 ga watan Dhul Hajj a kowace shekara.
Yin Layya wata hanya ce ta bin umarnin da yin biyayya ga mahalicci. Don haka da’a ga Allah da iyaye da kuma shugabannin al’umma ita ce ingantacciyar hanyar sadaukarwa. A fahimta sadaukarwa ba ta tsaya kadai ga bin umarnin yin layya ba ne, a’a, ya kunshi yin biyayya ga umarnin Allah SWT da duk wata sadaukarwa don ci gaba jama’a.  Samar da ingantaccen shugabanci da zai amfani da jama’a da kasa na daya daga cikin ingantacciyar sadaukarwa.
Kamar yadda shari’a ta tanadar ana so duk wanda ya samu ikon yin layya sai ya yi sadaka ga makwafta da kuma sauran al’umma musamman ma marasa karfi. A lokacin sallar layya ana so a rika ziyartar juna hakan zai yaukaka zumunci ya samar da hadin kai, ya kuma sanya a yafe wa juna laifuffuka da aka aikata wa juna.
Shugabanci da ke cike da tawali’u da kamala da gaskiya da adalci da kuma rungumar jama’a wasu halaye ne da ke tabbatar da ingantacciyar sadaukarwa. Wadannan halaye a yanzu sun yi karanci a tsakanin shugabanni da kuma talakawan kasar nan. Don haka ya kamata zababbun shugabanni da wadanda aka nada da na wucin gadi da na addini su rika amfani da wadannan halayen don dawo da kasar nan turba daidai don a samu ci gaban tattalin arziki da bunkasar kasar nan.
Muna fata gwamnati za ta yi amfani da wannan lokacin don daukar kwararan matakai da za su magance talauci da cin hanci-da-rashawa da kuma rashin aikin yi da suka hana kasar nan sakat. Yin hakan zai rage radadin talaucin da ’yan Najeriya suka samu kansu a ciki. Ya kamata kowane shugaba ya rika sanya al’ummarsa a zuciya, ya rika yi musu abubuwan da za su inganta rayuwarsu.  ’Yan siyasa su daina batar da matasa ta hanyar raba kawunansu don biyan bukatar kashin-kansu.
Bakaken abubuwa sun faru a Najeriya a shekarun da suka gabata musamman ma matsalar tsaro da ta hana kasar nan motsawa nan-da-can, don haka gwamnati ta tashi tsaye wurin magance matsalar da ke neman kai kasar nan kasa.  Ta yi amfani da hanyoyin hikima ba na nuna karfi ba ciki har da tattaunawa wurin kawo karshen matsalar tsaro. Haka duk wata kungiya ko mutum da ke da wani korafi to ya bayyana shi ta hanyar hikima ba amfani da makamai ba. Tayar da kayar baya ko tayar da zaune tsaye ba su ne sahihan hanyoyin bayyana rashin adalci ko take hakki ba. Hakan sai dai ya kara ta’azzara al’amarin ba wai samar da bakin zaren matsalar ba.
Duk wadansu hanyoyin da za su samar da zaman lafiya su ake so, a kuma yi amfani da sakonnin da za su kawo zaman lafiya a kowane yanki.
Ya kamata Musulmi su yi amfani da darussan sallar layya wajen kawo zaman lafiya a kasar nan, su kuma yi amfani da wadannan darussan wurin yi wa shugabanni addu’a don su samar da kyakkyawan shugabanci.
A karshe muna fata Allah Ya maimaita mana cikin koshin lafiya da wadata da kuma kwanciyar hankali. Barka da Sallah!