✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barka Da Sallah, Barka Da Sabuwar Rayuwa

Ya ma’abuta bibiyar filin Sinadarin Rayuwa, ina taya mu Barka Da Sallah, musamman bayan da muka samu dacewa da azumtar muhimmin wata na Ramadan. Kasancewar…

Ya ma’abuta bibiyar filin Sinadarin Rayuwa, ina taya mu Barka Da Sallah, musamman bayan da muka samu dacewa da azumtar muhimmin wata na Ramadan. Kasancewar watan da muka baro baya, wata mai albarka, wanda ke dauke da darussa masu yawa. To kuma, a rayuwarmu ta yau da kullum, fita daga watan, tana yi mana ishara ne da shiga sabuwar rayuwa. Saboda haka, a yau, darasinmu zai fuskanci nazari ne da tilawar irin rayuwar da ya kamata mu tsinkaya, a sauran watannin da za su gabace mu.
Wani babban darasi da za mu iya dauka daga watan da ya gabata shi ne, muhimmancin da ke tattare da lokaci. Kamar yadda muka dage, muka takarkare muka yi ayyukan alheri a cikin watan Ramadan, to fa mu gane, mun yi amfani da lokacin ne yadda ya dace. Ke nan, a yau da muka fita daga watan na Ramadan, to kamata ya yi a ce mun shiga sauran watanni da sabuwar rayuwa, yadda za mu ci gaba da ririta lokacinmu muna aikata ayyukan alheri.
Irin yadda muka kame bakunanmu daga muggan kalamai, kamar karya da gulma da zunde da sauransu a lokacin azumi, to yau da muka shiga sabon wata, to kamata ya yi mu fuskanci sabuwar rayuwa. Kada kuma mu ce za mu bata lokacinmu da miyan bakinmu wajen furta kalaman da ba su dace ba. Lallai ne yadda muka yi watsi da karya a lokacin azumi, to yanzu ma mu kaurace mata. Duk abin da bakinmu zai furta, mu tausa, mu tabbatar da cewa kalamai ne masu fa’ida, wadanda za su amfane mu da sauran al’umma. Kada mu ce za mu rika zubar da maganganu marasa muhimmanci, wadanda za su illata mu kanmu da kuma sauran al’umma. Ke nan mun fita daga watan Azumi, mun shiga sabuwar rayuwa, kamar dai jaririn da aka haifa sabo, ya shigo duniya domin fara gudanar da sabuwar rayuwa.
Akwai da dama daga cikinmu da muka kasance muna aikata munanan halaye kafin shigowar watan Ramadan. Da Allah Ya yi mana katarin shiga watan, sai muka sanya wa kawunanmu takunkumi, muka daina aikata su, saboda abin da aka bukata ke nan a Ramadan. To ga shi Ramadan ya yi mana bankwana, mun fita daga gare shi. Yanzu kuma me ya kamata mu yi, a sabon watan Sallah da muka shiga? Abin da za mu yi shi ne, mu gudanar da sabuwar rayuwa, kamar yadda muka koya a watan da ya gabata.
Kafin azumi, mutum ne ya kasance mai shan giya, mai shan taba, mai shan wasu abubuwa na sa maye, kamar kwaya da sauransu. Lokacin azumi, wata guda cur, sai mutum ya daina shan wadannan ababe, kuma babu abin da ya same shi. A sanadiyyar haka, ruhinsa ya gyaru, tarbiyyarsa ta kintsu. Ke nan ya koyi wani abu sabo a rayuwarsa, wanda ake fatan ya ci gaba a haka.
Haka ya kamata mutum ya kasance a yanzu da ya samu kansa cikin sabon wata, ya kamata ke nan ya yi watsi da waccan dabi’a tasa ta baya kafin azumi. A yanzu ma, kamar yadda ya yi a azumi, sai ya ci gaba da kaurace wa shan giya, kada ya ce kuma zai sha kwaya da sauran kininta. Idan ya yi haka, babu shakka zai samu sabuwar rayuwa. Ke nan darussan da ya dauka daga azumi, sun yi tasiri ke nan a rayuwarsa.
A wannan sabon wata, wanda daga gare shi ne muka fita daga watan Ramadan, kamata ya yi ya kasance mana sabon tambari, wanda zai doka mana kyawawan misalai. Duk wani abu da muka bari marar kyau a lokacin azumi, to mu bar shi a cikin wannan sabon wata, da ma sauran watanni masu zuwa a rayuwarmu.
Idan muka yi haka, mun girbi babbar riba, mun ci jarabawar da aka yi mana a watan Ramadan. A watan na baya, mun kasance tamkar dalibai ne, wadanda suka shiga makaranta, suka koyi darussa da gabubban jikinsu. A wannan wata kuwa da sauran watanni masu biye masu a rayuwarmu, lokuta ne da za mu dibiya ilimin da muka samu. Ke nan sauran watanni za su kasance mana tamkar lokutan rubuta jarabawa – jarabawar canja sabuwar rayuwa.
Mun koyi daina fadar karya a azumi sai gaskiya. Yanzu ma sai mu ci gaba da haka a sauran lokuta. Mun daina yin sata da ha’inci da handama da babakere a cikin azumi. Yanzu ma sai mu kasance masu amana, ba maha’inta ba, mu kasance masu gaskiya, ba barayi ba. Wannan ita ce sabuwar rayuwar da ta kamace mu a sauran watannin bayan Ramadan.
Mun koyi cewa zina da sauran alkaba’i irinta ba su da kyau, kuma ba mu aikata su ba a cikin Ramadan. A yanzu da Ramadan ya wuce, muka shiga sabon wata, to kuwa mun shiga sabuwar rayuwa, yadda za mu kasance sababbi, masu sababbin halaye. Za mu ci gaba da kaurace wa zinace-zinace da sauran dangoginta, kamar dai yadda muka yi a Ramadan.
A Ramadan, mun kasance mutane masu kana’a, masu da’a da kyawawan halaye. Mun kasance masu tausayi da jinkan juna. Muna taimakon fakirai da marasa galihu. Ga shi yanzu lokacin Ramadan ya shude, mun shiga sabon wata. Mu kasance masu ci gaba da wadannan kyawawan halaye, ta yadda za mu ci gaba da kasancewa sababbi, masu sabuwar akida da sabuwar rayuwa.
Allah Ya sa mu dace, amin. Barka Da Sallah, Barka Da Sabuwar Rayuwa!