Barcelona ta sha da kyar a gidan Villarreal yayin fafatawar da suka yi yau Lahadi a wasan mako na uku a La Liga.
Barcelona ce dai ta doke Villarreal da ci 3-4 a filin wasa na Estadio de la Ceramica.
- Satar ɗanyen man fetur ce ta ƙara tsadar rayuwa a Najeriya — Nuhu Ribadu
- Shugaban Amurka ya buƙaci ganawa ta musamman da Tinubu
Barcelona ce ta fara cin kwallaye biyu cikin minti 15 da fara tamaula ta hannun Pablo Gavira da kuma Frenkie de Jong.
Daga baya ne Villarreal ta zare daya ta hannun Juan Foyth a minti na 26, sannan Alexander Sorloth ya farke na biyun, saura minti biyar su je hutu.
Bayan komawa zagaye na biyu ne Villareal ta kara na uku ta hannun Alex Baena.
Daga baya kuma Barcelona ta farke kwallo ta hannun Ferran Torres, sannan Robert Lewandowski ya ci na hudu saura minti tara a tashi daga karawar.
Barcelona mai rike da La Liga ta fara tashi 0-0 a wasan farko da ta bude kakar bana a gidan Getafe ranar 13 ga watan Agusta.
Kungiyar Camp Nou ta doke Cadiz 2-0 a wasan mako na biyu a babbar gasar tamaula ta Sifaniya ranar 20 ga watan Agusta.
Ranar 3 ga watan Satumba Barcelona za ta ziyarci Osasuna a wasan mako na hudu a La Liga.