✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Barcelona ta karbo aron Adama Traore daga Wolves

Kowa ya san Barcelona kungiya ce da take cikin ran Adama.

Kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta karbo aron dan wasan Wolves Adama Traore nan da zuwa karshen kakar wasanni ta bana.

Barcelona za ta rika biyan dan wasan kudadensa sannan kuma a yarjejeniyar da aka cimma za ta iya sayan shi kan fam miliyan 30 a lokacin bazara.

Barcelona ta samu nasarar dauko dan wasan ne a rige-rigen da ta yi da Tottenham, wadda kocinta Antonio Conte ya yi hankoron dauko shi.

Adama Traore

Watanni 18 ne suka rage wa Traore a kungiyarsa ta Wolves kuma babu wata yarjejeniya a kasa ta neman ya tsawaita kwantaraginsa da kungiyar, lamarin da ya kai ga ta fara neman kai da shi.

“Kowa ya san Barcelona kungiya ce da take cikin ran Adama kuma wannan komawar da zai yi cikar burinsa ne,” in ji shugaban bayar da atisaye na Wolves, Scott Sellars.

Traore ya fara kwallonsa ne a Barcelona gabanin ya koma Aston Villa a 2015.

Ya kuma shafe shekara biyu a kungiyar kafin daga bisani ya koma Wolves a 2018.