✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barcelona ta fara yunqurin xauke Isco daga Madrid

Kulob xin FC Barcelona na Sifen ya fara tunanin xauke xan qwallon tsakiya a kulob xin Real Madrid Isco. Kulob xin ya ce ya fara…

Kulob xin FC Barcelona na Sifen ya fara tunanin xauke xan qwallon tsakiya a kulob xin Real Madrid Isco. Kulob xin ya ce ya fara tunanin xauke xan qwallon ne ganin yadda kwantaraginsa za ta qare ne a shekarar 2018 a Madrid amma Madrid xin tana jan qafa wajen sabunta masa kwantaragi da hakan zai ba kulob xin damar xauke shi ba tare da biyan ko sisin kwabo ba.
Sai dai rahotanni sun nuna xan qwallon ya fara tattaunawa da mahukunta kulob xin Madrid a yanzu a qoqarin sabunta masa kwantaragi.
Barcelona ta lasa wa Isco zuma ne a baki inda ta nuna xan qwallon ne zai gaji Andre Iniesta idan ya amince da tayin da suka yi masa.
Kafar yaxa labarin wasanni ta Goal.com ta nuna, FC Barcelona tana neman Isco ne don ya maye gurbin Andre Iniesta da ya kama hanyar yin ritaya inda zai riqa buga wasa a kan kari ba kamar yadda kocin Madrid Zinedine Zidane yake ajiye shi a benchi a mafi yawan lokuta ba