Kungiyar ’yan kabilar Igbo ta la’anci Kungiyar Neman kafa kasar Biafra (IPOB), musamman na bata sunan Fulani makiyaya a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya.
Gamayyar Kungiyoyin Kwararrun Kudu Maso Gabas a Ciki da Wajen Najeriya (CSEPNND), ta ce Fulani makiyaya da ma wadanda ba makiyaya ba na da cikakken ’yancin zama da ko’ina a Najeriya kamar kowane dan kasa.
- Rufe masallaci: Sheikh Abduljabbar ya yi raddi ga Gwamnatin Kano
- Maganin gargajiya ya kashe yara ya kwantar da mahaifiyarsu a Kano
- Matakan soyayya da bayaninsu dalla-dalla
- An girke jami’an tsaro a gidan Sheikh Abduljabbar
“Muna kira ga sojoji da sauran jami’an tsaro da su gaggauta kama duk masu alaka da ESN su fuskanci hukunci tare da ruguza daukacin kafofin a cibiyar tsaron ke da su,” inji CSEPNND.
“Fulani makiyaya masoya zaman lafiya na da ’yancin zama a duk yankin Najeriya da suke so kamar sauran ’yan kasa ba tare da takura ba, kamar yadda dokar kasa ta tanadar,’’ inji Shugaban CSEPNND Farfesa Chika Madumere.
Ya yaba wa al’ummar Hausa Fulani a fadin Najeriya bisa kawaicin da suka nuna duk da yunkurin Shugaban IPOB Nnamdi Kanu na yi wa jama’arsu cin kashi a yankin Kudu maso Gabas.
“Muna jinjina ta musamman ga ’yan uwanmu Hausa Fulani a yankunansu da sauran wurare bisa rashin daukar doka a hannunsu da suka yi duk da irin tunzurin da Kanu da mabiyansa ke yi,’’ inji shi.
‘Kungiyar IPOB ‘yar ta’adda ce’
Shugaban na CSEPNND, ya tunatar da al’ummar Igbo cewa kotu mai cikakken iko ta riga ta ayyana IPOB a matsayin haramtacciyar kungiyar kuma ’yar ta’adda.
A don haka, ya yi tir da abin da Nnamdi Kanu da ’ya’yan IPOB ke yi wa Fulani da ke nuna cewa kabilar Igbo al’umma ce mai tashin hankali, mara karmaci kuma mai kyamar baki.
Ya kuma la’anci haramtaciyar kungiyar tsaro ESN da Nnamdi Kanu ya kafa, yana mai cewa al’ummar yankin Kudu maso Gabas masoya zaman lafiya da kuma maraba da baki ce.
“Muna kira ga sojoji da sauran jami’an tsaro da su gaggauta kama duk masu alaka da ESN su fuskanci hukunci tare da ruguza daukacin kafofin a cibiyar tsaron ke da su,” inji CSEPNND.
Ta jaddada cewa hadin kan Najeriya abu ne da babu zabi, a don haka ya yi kira ga daukacin al’ummar Igbo a Najeriya da ketare da su juya wa Nnamdi Kano baya.
Kungiyar ta kara da cewa babu yadda za a yi wasu tsiraru su balle daga cikin halastacciyar gwamnati su kafa tasu.
Don haka “Jami’an tsaro da su gaggauta kama duk masu alaka da ESN su fuskanci hukunci tare da ruguza daukacin kafofin a cibiyar tsaron ke da su.
“Muna bayyanawa karara cewa abin da Kanu ke yi a baka ko a aikace, yana yi ne ba da amincewar yankin Kudu maso Gabas ba, don haka a yi watsi da shi.
“Muna kuma nisanta kanmu da ma daukacin al’ummar Kudu maso Gabas daga duk wata barazana da ake yi wa Fulani makiyaya a yankin; a koyaushe muna goyon baya cikakken ’yancin dan kowane dan kasa na zama da gudanar da halartaciyar rayuwa a duk inda ya zaba a fadin Najeriya.”