✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barayin fasaha na neman durkusar da harkar fim – Safna Maru

Safna Aliyu Maru, jarumar fina-finan Hausa ce. Duk da cewa tana da karancin shekaru, a yanzu ta fara shirya fina-finai da kudinta. A hirarta da…

Safna Aliyu Maru, jarumar fina-finan Hausa ce. Duk da cewa tana da karancin shekaru, a yanzu ta fara shirya fina-finai da kudinta. A hirarta da Aminiya ta bayyana dalilin da ya sa ta fara harkar fim, nasarorin da ta samu, kamar kuma yadda ta kuma fadi dalilin da ya sa za ta kashe mukadan kudi wajen shirya fim a kan cin amana. Ga yadda tattaunawar ta kasance:

Yaya kike ji kasancewarki jarumar fina-finan Hausa duk da karancin shekarunki?

Zan iya cewa masana’antar fina-finan Hausa kamar gida ce a wurina kasancewar ina tare da masu shirya fina-finai tun kafin in zama jaruma. Wadansu suna cewa shekarata 25 amma a gaskiya shekarata 21. An haife ni a Kano, na kuma taso a Kano. Ta bangaren yadda nake ji sakamakon kasacewata jaruma kuwa, sai in ce ina cikin farin ciki da jin dadi, duk da cewa ni yarinya ce karama idan ka kwatanta ni da sauran jarumai mata da kuma da furodusoshin da daraktocin da ke cikin masana’antar.

Masu ruwa da tsaki a masana’antar sun taimaka mini, domin suna ba ni taimakon da nake bukata, don a gaskiya ba don taimakona da suke yi ba da ba zan kai matsayin da nake a kai ba. Zan iya cewa ni shalele ce a wurinsu, domin ina da dangantaka da ’yan fim irin na ya da kanwa, wa da kanwa da uba da ’ya, domin komai nake yi akwai wanda yake zama jagorana.

 

Fim dinki mai suna ‘Fuska Biyu’ ya samu karbuwa, yaya aka yi kika kai ga yinsa?

Fim din yana kasuwa, kafin in kai ga yinsa, sai da na natsu na yi tunani in zo da wani jigon da ya bambanta da sauran jigogin da aka saba gani a fina-finan Hausa, wanda ya rubuta labarin kwararre ne wajen tsara labaran Hausa, na kashe kudi sosai a fim din, kuma na samu abin da nake so. Jama’a da dama suna tambaya yadda na kashe makudan kudi wajen shirya fim mai inganci da kuma kayatarwa da fadakarwa, sai in fada musu nasara daga Allah ta zo, amma dai na tsaya na yi shiri sosai.

 

Mene ne gaskiyar jita-jitar da ake watsawa cewa a yanzu kina shirin kashe miliyoyin Naira a kan sabon fim dinki mai suna ‘Nazeer Zahrah?’

To, ban gane abin da suke nufi na cewa babban kasafi ba, kodayake ya danganta da yadda mutum ya fahimci babban kasafi a wurinsa, amma dai zan iya cewa fim din zai lashe miliyoyin Naira, fim ne da ya kunshi manyan jarumai maza da mata masu aji a Kannywood.Mene ne jigon labarin?

Fim ne mai dauke da jigon cin amana da kuma sakamakon da yake haifar wa mai yinsa da kuma al’umma musamman a kan cin amanar da ake yi wa masoyi na gaskiya.

 

Me ya sa fim din a kan cin amana?

Wadansu za su dauka cin amana karamin abu ne, kuma abu da ake yinsa ba tare da tunanin laifi ko abu mai muni ba ne, daurewa wajen guje wa cin amana da kuma rashin hakuri idan an ci mana amana ba abu ne da mutane suke iya yi ba, da yawa mutane suna cin amana amma sai ka ji an yi shiru kamar ba wani abu aka yi ba. Abu ne da ya kamata mutane su guda. Don haka fim dina mai suna ‘Nazeer Zahrah’ ba wai kawai yana dauke da jigon cin amana ba ne, yana dauke da batun soyayya na daban.

 

Wadanne jarumai ne za su fito a cikin fim din?

Akwai jaruman da suka hada da Ali Nuhu da Sadik Sani Sadik da Isa Adam (Feruz Khan), a bangaren mata kuma akwai Asma’u Sani da Safna Aliyu da Hafsat Idris da sauransu.

 

Kamar zuwa yanzu fina-finai nawa kika yi?

A bisa ga lissafina na fito a fina-finai sun kai 20, wadanda suka hada da ’Yan Mata da ‘Daren Zalunci’ da ’Yan Boarding’ da ‘Fuska Biyu’ da ‘Zangina’ da sauransu, amma ina da yakinin cewa sabon fim dina ‘Nazeer Zahrah’ ya bambanta da su.

Ga bangaren nasarorin da kika samu fa?

Na fito a fina-finai masu yawa, na tara masoya, ina samun alfarma dalilin yin fim, na kai ga shirya fina-finai na kaina da sauransu. Masu iya magana sun ce al’umma rahama ne, ko jama’ar da suka san ni da kuma masoyan da nake da su abin alfahari ne a wurina, hakan babbar nasara ce a wurina.

 

Wadanne matsaloli kika fuskanta a harkar fim?

Gaskiya ban fuskanci matsaloli ba, kamar yadda na fada muku a baya  kowa nawa ne a Kannywood, kuma komai nake yi a akwai masu ba ni shawari, ba na yin gaban kaina, kuma ina kiyaye duk wani abu da na san zai bata mini suna ko ya zubar mini da mutunci.

 

Ko kin fuskanci matsala daga wurin iyaye ko abokai ko ’yan uwanki bayan sun fahimci za ki shiga Kannywood?

Gaskiya ban fuskanta ba, domin kamar yadda na fada maka ina cikin masana’antar tun kafin in fara fim, na san su, su ma sun san ni, kuma kowa nawa ya san wadansu daga ciki, ya san mu’amalarsu, don haka babu matsalar da na fuskanta.

 

Wane kira kike da shi ga masoyanki?

Ina so su ci gaba da yi mini addu’a da kuma sauran jaruman da suke Kannywood, idan mun yi kuskure kada su hantare mu, su gyara mana cikin hanya mafi dacewa, idan mun yi abu mai kyau su yabe mu, sai mu ji karfin gwiwar ci gaba da faranta musu. Sannan su daina sayen fina-finai a wurin masu satar fasaha, hakan na mayar da mu baya, yana kuma neman kassara masana’antar.