An gargadi mazauna Karamar Hukumar Mai’adua a Jihar Katsina kan sata ko lalata amfanin gonar mutane.
Mai Shari’a Zayyana Ibrahim Dan Ali, na kotun Majistare da ke garin Daura, ya ce barayin amfanin gona za su fuskanci daurin shekara biyar a gidan yari, ba tare da rangwame ba.
- An kama tirela cike da shanun sata
- A aikace ya kamata a magance matsalar tsaro —Sarkin Musulmi
- Mutum 154 sun bace bayan kifewar jirgin ruwa a Kebbi
“Duk wanda aka kama da laifin shiga gonar wani ba da izini ba, za ai masa daurin wata shida ko tarar N25,000 ko kuma duka,” a cewarsa.
Alkalin ya ce masu lalata amfanin gona kuma ana musu daurin kasa da shekara biyu ko tarar N70,000 ko kuma duka biyun.
Ya yi gargadin ne a taron kara wa juna sani da aka shirya a yankin Mai’adua, Koza da Yadin, kan yadda bata-gari ke lalata amfanin gonaki.
Shi ma da yake nasa jawabin, Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar, Yau Umar Gwajo-Gwajo, ya ce yanzu manoma suna sayar da amfanin gonarsu tun kafin su girbe saboda tsoron sata.
“Tabbas wannan matsala ta satar amfanin gona na iya kawo matsalar karancin abinci.
“Kun ga yadda manoma suka karbi taron da muhimmanci saboda yadda matsalar ta shafe shekaru tana damun su,” cewar Gwajo-Gwajo.
Kwamishinan ya ce an shirya taron ne don tunatar da jama’ar yankunan kan muhimmancin bin doka da kuma kiyaye ta.