✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barayi sun yi garkuwa da mutum biyu da sace shanu 17, awaki 30 a Katsina

A daren jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Ruwan Dorawa da ke karamar Hukumar Dutsinma ta jihar Katsina, inda suka sace shanu…

A daren jiya ne wasu ‘yan bindiga suka kai hari kauyen Ruwan Dorawa da ke karamar Hukumar Dutsinma ta jihar Katsina, inda suka sace shanu 17 da awaki 30, wakilinmu ya samu rahoton cewa, barayin sun shiga kauyen ne da tsakar daren jiya Laraba sannan suka yi awon gaba da dabbobin.

Daga bisani kuma ‘yan bindigar sun shiga kauyen Gidan Mai Pampo, inda suka yi garkuwa da mutum biyu wadanda suka hada da Alhaji LG, da wata mata mai suna  Hajiya Zainab Zaria.

Sai dai Hajiya Zainab Zaria, ta tsere ta dawo kauyen daga hannun su.