✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Barayi sun kona kayayyakin wani coci a Kaduna

Wadansu da ake zargin barayi ne sun shiga cocin Saint Augustine da ke Layin Chawai a Tudun Wada Kaduna inda suka yi sata tare da…

Wadansu da ake zargin barayi ne sun shiga cocin Saint Augustine da ke Layin Chawai a Tudun Wada Kaduna inda suka yi sata tare da kona wasu kayayyakin cocin.

Lamarin wanda ya faru da misalin karfe 11: 30 na daren ranar Juma’a da ta gabata ya tayar wa gwamnati hankali bayan yaduwar labarin a dandalin sada zumunta.

Aminiya ta ziyarci cocin inda ta samu ganawa da daya daga cikin  masu gadin cocin wanda ya bukaci a sakaya sunansa, inda ya shaida mata cewa wadansu batagari ne da ba a san ko su wane ne ba suka yi nasarar sace wayayoyin lantarki a cocin.

Ya ce a lokacin da suka zo masu gadin dare ba su iso ba wanda hakan ya sa suka samu damar cin karensu babu babbaka.

“Babu wanda ya san ko su wane ne ko mece ce manufarsu amma dai sun sace wayoyin wuta da tagogi daga bisani suka kunna wuta a cikin cocin tare kuma da kona kayayyakin da ke kan mumbarin cocin.

“Daliban Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Kaduna wadanda dakunan kwanansu ke jikin cocin ne suka taimaka wajen kashe wutar bayan sun hango wuta na ci daga cikin cocin da daddaren,” inji shi.

Aminiya ta samu labarin cewa jami’an tsaro ciki har da ’yan sanda da sojoji da DSS sun je cocin domin gane wa idanunsu abin da ya faru.

Kuma biyu daga cikin masu gadin cocin da ya kamata su yi aikin dare a ranar da abin ya faru na tsare a wajen ’yan sanda domin amsa tambayoyi.

Tuni Gwamnan Jihar Kaduna Malam Nasir El-Rufa’i ya kai ziyara cocin, inda ya jajanta wa mahukuntan cocin da masu ibada a ciki da kuma sauran wadanda abin ya shafa, kuma ya ce gwamnati za ta biya asarar da aka yi. Sannan ya tabbatar da cewa za a gudanar da bincike domin bin kadin lamarin.

Gwamnati ta kuma yaba wa shugabannin cocin a kan kokarin da suka yi na gudanar da ibadunsu a ranar Lahadi cikin kwanciyar hankali duk da abin da ya faru wanda haka alama ce ta jajircewa tare da kaunar zaman lafiya.