✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

barawon babur

Wani ne matarsa ta haifi jaririn da bai zo da rai ba a asibiti, sai ya samu babban kwalin biskit ya saka gawar jaririn a…

Wani ne matarsa ta haifi jaririn da bai zo da rai ba a asibiti, sai ya samu babban kwalin biskit ya saka gawar jaririn a ciki, ya dora a kan babur. Ya bar babur din a kafe, ya je cikin asibiti domin ya sallami likita. Ko da ya dawo sai ya samu an sace babur da gawar da ke cikin kwalin. barawon yana tafiya sai ya hadu da ’yan sanda, ya ciro Naira dari ya ba su, ya ce: “Oga ina sauri ne!” Wani dan sanda ya ce: “To ka ba mu biskit din mana.” barawo ya bude kwalin da nufin ciro biskit, sai ga gawar jariri kwance. Sai barawo ya ce: “Wallahi oga ni ba barawon yara ba ne, ni barawon babur ne!”
Daga Sunusi NNPC, 08034367040