✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ɓarawo ya haɗiye ɗan kunnen Naira biliyan ɗaya

’Yan kunnayen da aka sace, waɗanda darajarsu ta kai Dalar Amurka 769,000.

Jami’an tsaro sun jiran kayan ado na ’yan kunnayen zinare su wuce ta na’urar binciken fasinjan jirgin sama kafin a gano kayan da aka sace a hukumance.

An kama wani mutum mai shekara 32, mai suna Jaythan Lawrence Glider bisa zargin satar ’yan kunne biyu na zinare na sama da Dalar Amurka 769,000 — kwatankwacin Naira biliyan 1 da miliyan 177 da dubu dari 615 da 840 daga wani babban kantin da ke Millenia a birnin Orlando da ke Jihar Florida a Amurka a ranar 26 ga Fabrairu.

A cewar sashen ’yan sanda na Orlando, Glider ya dauki matakin da ba a saba gani ba na haɗiye ’yan kunnayen da ya sace.

A cewar rahoton ’yan sanda da kafar yada labarai ta WFLA, Glider ya yi amfani da damar shiga sashen kayan ado masu tsada a kantin Tiffany & Co a ranar 26 ga Fabrairu ta hanyar nuna matsayin wakilin ɗan wasan ƙwallon kwando na Orlando Magic.

Rahotanni sun ce wannan dabarar ta ba shi damar shiga cikin sashen manyan kayayyaki masu tsada, inda ya yi awon gaba da su.

An kai shi kurkuku bayan an tsayar da motarsa a kan hanyar Interstate 10 a gundumar Washington.

An kama shi ne bisa zargin kin amincewa da kama shi, baya ga wasu fitattun sammaci guda 48 da aka gano daga Colorado.

Al’amura sun zama abin mamaki lokacin da Glider ya tambayi ma’aikatan gidan yarin, “Shin za a tuhume ni da abin da na hadiye?”

Wannan shigar da bincike da aka yi ya kai ga duba jikin mutumin, inda aka gano wasu abubuwan da hadiya a cikinsa.

Hukumomin sun yi zargin cewa, waɗannan ’yan kunnayen da aka sace, waɗanda darajarsu ta kai Dalar Amurka 769,000 (kwatankwacin Naira biliyan 1 da miliyan 177 dubu dari 615 da 840), inda aka yi zargin Glider ya haɗiye.

Jami’an tsaro a yanzu suna jiran gano kayan ta hanyar na’urar bincike.

Kamar yadda aka sani, haɗiye ƙananan abubuwa kamar ’yan kunnaye bai fiya haifar da babbar illa ba.

A cewar ƙwararrun likitocin, idan abin ya gaza inci ɗaya ko kuma ƙasa da inci 2, to zai iya wucewa ta hanji ba tare da haifar da wata matsala ba.

Glider yana da tarihin matsalolin shari’a, inda aka ba shi sammaci guda 48 a Colorado musamman ma, an kuma tuhume shi da laifin yin fashi a wani kantin Tiffany & Co da ke Texas a cikin shekarar 2022.

Bayan kama shi a baya-bayan nan, Glider na fuskantar tuhumar babbar sata a matakin farko da fashi da abin rufe fuska.