Gwamnatin kasar Haurobiya ta bullo da sabon shirin girgie rumfar Barau dan canji, ta yadda za a karya lagonsa wajen hada-hadar musayar Haur da Dalolin Amurkawa da Fama-faman Ingilawa da riyalan Sawun-diyyar Larabawa da dinari da dirhamin Larabawa. Wannan sabon tsarin tsiyata barau dan canji, ya tanadi daukacin masu hada-hadar musayar Hauro da damin kudin kasashen waje su adana Hauro malala kofar hanci da babban lauje a asusun ajiya, wanda ba zai haifar da wata fa’ida ba; kodayake ana ganin wata garkuwar asara ce.
Wannan tsarin tsiyata iyalan Barau dan canji, GwamnanBaban Asusun Haurobiya ne ya bullo da shi, musamman don ya nuna ya fi magabatansa iya aika-aika. Wato dai Sallau Lado da Masanin Sisi-da-Sisi ba su kware da aika-aika ba, domin har suka kammala wa’adin jan ragamarsuba su kayyade wa iyalan Barau adadin Hauron ya kamata su rika hada-hada su ba, matukar dai suna bai wa gwamnati haraji, sun biya kudin rajistar hada-hadar kasuwancinsu. Ko dai mece ce manufar girgide rumfar Barau dan canji da ake yi a kasar nan, masu hankali a jikinsu, sun tabbatar da cewa wani rukuni na al’umma ake shirin tsiyatawa, a kora wajen sana’ar kashe fatari da zaman dirshan a garuruwansu, musamman ma idan an yi la’akari da cewa mafi yawan masu hada-hada a rumfar Barau dan canji, Arewatawan Haurobiya ne, sannan sun dade a wannan harka suna wadaka, don ba su taba tunanin za a iya yi musu katsalandan ba.
Shuigaban gungun masu hada-hada a rumfar Barau, Alhaji Gwaggwaban-dabe, yana ta kai kawo da zirya a tsakanin majalisar kasa da Babban Asusun Haurobiya, don ganin an tausasa wa ’yan uwansa, ta yadda kodai a rage yawan damin Hauron da Gwamnati ta yanke musu na garkuwar asara, ko kuma a kara musu wa’adin tara wa gwamnatin damin Hauro a asusu mara fa’ida.
Batu na ingarman karfen karafa, wannan tsarin tsiyata al’umma manufa ce ta kassara iyalan Barau dan canji da nuna wariyar bangaranci. Irin wannan manufa ta Gwamnatin Haurobiya ana ta aiwatar da ita don cutar da Are-wawaye, a cewar AbdulKarimun nan na Birnin Dabo, wato Shugaban Rundunar Adalar-cici. Inda za a iya fasko cewa Haurobiyawan Arewacin Haurobiya sun zama Arewawaye, shi ne, yadda aka hana sana’ar cabawa da zabarin baburido a tituna, alhali ba a yi wa masu jini a jika tanadin komai ba; an kyale kowa ya je ya ji da kansa, ta yadda in ma samartakar kusu za ka yi don ka tsira da rayuwa babu wanda ya damu. Kai hatta kamen da aka yi wa Arewatawa a yankin Kudancin Haurobiya, an aiwatar da shi da manufar kada wata shorido ko kurkuridon ta rika zirga-zirga a tsakanin Arewaci da Kudanci, matukar ba mallakar Kadawa ba ce. Bisa la’akari da wadannan al’amura da ke faruwa a kasa, ya kamata Barau dan canji da iyalansa su shiga taitayinsu.
Da iyalan Barau dan canji a masu kunnen kashi ba ne, wannan tsarin tsiyata al’umma da aka bullo musu ya isa a ce sun yi hannun taguwa da Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge, domin ta jirga su. Sannan Ja-gabansu, Alhaji Gwaggwaban-dabe, ya zauna ya yi karatun wasikar jakin dawa da na gida kan yadda za su rika balaguro a tafarkin zamani. Don haka akwai bukatar yin hadakar gungun masu hada-hada a rumfar Barau dan canji; da saka jari a asusu-asusun Haurobiya. Uwa-uba, ku shiga kasuwar ririta jaririn jari ta kasar Haurobiya, inda za a rika dama da ku a kodayaushe.
Sai dai wani hanzari ba gudu ba, ni idan na mallaki tarin dukiya babu yadda za a yi in yi hada-hada a rumfar Barau dan canji. Babban abin da zan yi shi ne sana’ar mutanen Bankin-koko, kodayake ba ina nufin ku tafi kasar Tayar-Landan ba, a’a, wato ku yi koyi da sana’arsu ta na-duke, inda suke shuka samfarera, su kuma yi musayarta da kasashen duniya, ta yadda za a jinka musu Dalar Amurkawa da Fama-faman Ingilawa da Riyalan Sawun-diyyar Larabawa da Dinari da dirhamin Larabawa. Abin da nike nufi akwai tasgaro a cikin cinikin Hauro da Hauro, amma shi cinikin tsabar hatsi da damin Hauro ko ba ni gishirin beza in baka manda, al’amari ne da ke da tushe a kundin labaran da, da na yanzu. Kun ga ke sai a bambance tsakanin tsaba da tsakuwa, wato tsakanin ’yan Hauren-Hatsi da Hauren-Danja. To iyalan Barau a yi azama, mai dan boto da sanda jirge da Gwamnatin Jatau mai sa-in-sa don Jona-tantin mulki ta himmatu wajen kassaraku. Sai a yi hattara.
Barau dan canji
Gwamnatin kasar Haurobiya ta bullo da sabon shirin girgie rumfar Barau dan canji, ta yadda za a karya lagonsa wajen hada-hadar musayar Haur da Dalolin…