Bankin Raya Kasashen Afirka (AfDB) ya sake zabar tsohon Ministan Gona na Najeriya Akinwumi a Adesina a matsayin shugabansa.
Adesina zai jagoranci bankin a wa’adinsa na biyu na tsawon shekara biyar bayan zaben da aka gudanar a ranar Alhamis, wanda shi ne kadai dan takara.
A ranar Laraba ya bukaci wa’adi na biyu, bayan shafe wata biyar ana kai ruwa rana kan zargin shugabancinsa da gazawa da kuma rashawa a bankin kafin ya wanke shi.
Sau uku sakamakon kwamitocin binciken zarge-zargen na wanke shi, bayan ya sauka daga mukamin domin a yi binciken na karshe wanda wani kwamiti mai zaman kansa ya gudanar.
A jawabin sa ranar Laraba domin neman tazarce wanda babu hamayya ya shaida wa taron shekara na AfDB cewa yana jagorantar bankin ne “domin hidimtawa da kuma sadaukar da kai.”
“Ina yi ne domin hidimta wa Afirka da bankinmu ba tare da wariya ba gwargwadon ikon da Allah Ya ba ni”, inji sanarwar da ya fitar.
Adesina shi ne dan Najeriya na farko da ya taba jagorantar Bankin Raya Afirka, daya daga cikin bankunan duniya guda biyar masu bayar da rance domin ci gaba.
Ana masa kallo a matsayin daya daga cikin manyan wadanda suka taka muhimmiyar rawa wajen habbaka tattalin arziki da ba a saba ganin kamarsu ba.
A watan Oktoban ya samu fice sosai bayan AfDB ya samo gudunmuwar Dala biliyan 115 wanda hakan ya ninka karfin jarin bankin da kuma darajarsa.