✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Banga-bangar Bankin-koko

A kasar Tayar-Landan cincirindon al’umma masu banga-banga a birnin Bankin-koko na shirin bankade Farar minister, mai Yawon-guloki, saboda kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma ya mamaye ko’ina.…

A kasar Tayar-Landan cincirindon al’umma masu banga-banga a birnin Bankin-koko na shirin bankade Farar minister, mai Yawon-guloki, saboda kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma ya mamaye ko’ina. Don haka ’yan adawa suka ce ko an ba su dawa ba za su yarda su shiga dawa ba. Ganin haka sai kawai Fararminista Yawon-guloki ta rusa majalisar kasa, wai za ta yi ’yan gyare-gyare irin na gyare da kurege, har ma ta yi nufin shirya zabi-sonka. Wannan takadama tsakanin masu adawa da Fararministar Bankin-koko ta jefa ni cikin ta’ajibi, tunda nasan Haurobiyawa ba za su iya katabus ba.
Tun a zamanin Shugaba ’Yar’bishiya na taba yin watsatsake mai taken  “Ta-zauna ko Ta-zame,” har  ta kai ga na doka muku misali da gunkin tsumburbura da aka taba yi wa bauta a birnin Dabo inda a halin yanzu ba dabo. ’Yan makaranta sai a ari faden Malam Tunau, kada a sake a kakaba wa kai tagiyar Malam Mantau. Muhimmin lamari dai, ya kamata a fasko cewa murgude zabi-sonka shi ke haifar da soye-soyen zukata, ind amasu mulkin mulaka’u ke kulla kawance da Malam Zalimu su yi ta musguna wa al’umma. Wannan badakala ita ta addabi mutanen kasar Tayar-Landan, don haka masu hankali a jika suka ce lallai mu  yunkura, mu yi wa tufkar hanci.
’Yan makaranta, masu koyon watsattsake da buda wagagen littattafai a wannan farfajiya ta Dodorido da ke cikin Amintattar jarida ta kasar Haurobiya, kun san na dade ban yi muku jarabawa ba. To ga tambayoyi nan kamar haka: Wane ne ya yi samartakar kusu, ya sabi damin Hauro tiren-taliya madambaci? Na bijiro da tambayar domin in taimaka wa Masanin Sisi-da-sisi ya zakulo namijin burgun gafiya da ya wawushe dimbin damin Hauro daga lalitar Gwamnatin Haurobiya ya kai raminsa. Idan har kun fasko inda na tunkura a batuna, inda ganin bai kamata a ce Haurobiyawa sun shirya ‘Banga-bangar bankin-koko ba, don kada su banke In-gwangwaje-in-wala da Mace-dazane da uban tafiya Jatau Mai Gudun-loko. Domin babu tabbas cewa sun cacume damin Hauron ne a matsayin ca’ammas (kayan dundume kururu a birnin Tagadas). A’a, sun tafka wannan ta’asa ne don su samu na cukubus (kayan dundume kururu a lokacin bikin biyan non Abzinawa), musamman a lokacin da zabi-sonka ke karatowa, ta yadda za su samu damar murgude kuri’un al’umma a shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje.
Sanin kowa ne Loma-a-murde, wanda aka dora wa alhakin cafko masu kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma, ya zama muzuru Lami, don haka kuka ga ya gaza katabus, ya kyale kusu da jaba da gafiya suna ta wadaka. Shin akwai bukatar mu yi koyi ta al’ummar Tayar-Landan, mu yi Banga-bangar Bankin-koko? Sai ku bai wa kawunanku amsar wannan tambaya.
Ni dai kada ku yi mini mummunar fahimta, ku dauka cewa na dora wa Jatau Mai Sa-in-sa alhakin wawushe damin Hauro, inma shi ne ya tafka ta’asa, a kwanon tasa, ai sai da tallafin jiga-jigan Jam’iyyar Mai dan boto da sanda jirge. Kai a batu  na ingarman karfen karafa, wanda ya wawushe wadannan damin Hauron ba wani ba ne, illa mai kyakkyawar mummunar manufa. Shagaban da ya zari Hauro tiren-taliya, ya yi ne don ya nusar da Haurobiyawa yadda ake dambe da sasarin talalar talauci. Ya yi aika-aikar ne don ya zazzage asusun ilimi, ta yadda jam’in jama’ar jami’o’in Haurobiya za a daina koyar da watsattsake da buda wagagen litattafai; ya kuma tafka ta’asar ne don ya ahana al’umma walwalar uwar jiki a gidan Bokan Turai.
Ba tare da na cika ku da surutu kamar aku kuturu ko Kamfanin Dillancin Labarai na Reuters ba, ya kamata ku fasko cewa Loma-a-murde da Mai fari da idanu a cikin bakar kwalba duk suka nuna gazawa, wato dai sun zama muzuru da kyanwar Lami.
Yau dai Shugaban Majalisar Wakilan Rafkiya ya bayyana wa duniya cewa Shagaba Mai Gudun-loko shi yake bunkasa harkokin kwashi-kwaraf da dukiyar al’umma. Kowa ya ga yadda Jatau yake kare Santala kwaiduwa, wadda ta rarike lalitar hukumar kula da safarar tsuntsayen sama; ga Farfesun Gareji da tafka ta’asa a Ma’aikatar kula da Uwar-jiki, duk wadannan miyagu sun zama gafiya ta tsira da na bakinta ‘sauran gama-garin al’umma kuwa ko oho!
A matsayina na Direban alli, zan yi amfani da wannan dama don in gargadi Masanin Sisi-da-sisi ka daina bankade-bankade; ka yi likimo ka fice daga wannan gwamnati cikin lumana, domin ja-gabanta ba su da amana. Idan kuwa ka jajirce kan cewa sai an kawo sauyi, a hada-hadar sarrafa Hauro, wato a yi keke da keke, to sai ka yi koyi da Kamfanin Buga Amintattun jaridun kasar Haurobiya. Wannan kamfani da muke laluben na-koko a garin tako-tako da ke Haurubja bangaren Utako, ya yi dabarar hana mu Banga-bangar Bankin koko, ta hanyar jan na-zomonmu kan lallai: Mu daina ‘Yasar tankin yuyu, kuma mu rika kwankwadar  Nonon tankin yuyu.’  Duk wanda yake son fasko ma’anar Yasar tankin yuyu da shan nonon tankin yuyu, to sai ya fasakara kalmomi Ingilishi  na ‘Yes’ da ‘No’ bayan ya kanga gilashi, ya kuma ci kilishi. Ko kuma a rika bibiyar jaridun Kamfanin Buga Amintattun Jaridun Haurobiya a ji yadda suke ce wa ’yan kwadago kashedinku da karbar na-koko!

Ina son shiga makaranta
Assalamu alaikum. Bayan gaisuwa barkatai da fatan sarkin malamai yana kalau. Ina rubutu ne don neman izinin zama dalibi a wannan babban makaranta. Ni mai sha’awar karatun rubutun ka ne. Sunana Muhammad dan Muhammad dan Uthman, ni mutumin birnin ilmi ne, a kuma anguwar masu yanke hukunci (Anguwar Alkali). Lambar da za a kwada mini kira ita ce: 08038200973. Daga Muhammad Muhammad Uthman.

Ka tuntubi kungiyar dalibai ta kasa, ta cikin lambar bututun batutuwan kakakinsu, wato  zagae da madambaci da zagaye da kofar hanci da tsayuwa bisa kafa daya da kofar hanci da kofar hanci da karamin lauje da karamin lauje da zagaye da zagaye. To ka ji! Ehe!