Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, ya ce ko kadan ba ya shakkar faduwa zaben kujerarsa a 2023.
Makinde wanda ya yi rashin nasara a dukkan zabukan da tsaya takarar gwamnan jihar a shekarar 2007 da 2011 da kuma 2015, ya ce ko a yanzu al’ummar jihar Oyo suka nemi ya sauka daga kujerarsa zai tattara ina-sa-ina-sa ba tare wani jinkiri ba.
Gwamnan wanda ya bayyana hakan yayin wani taron Majalisar Yarbawa da aka gudanar a birnin Ibadan, ya kuma ce ba shi da wani uban gida na siyasa.
“A yau bari na fada muku ku ji, ba ni da wani uban gida a siyasa kuma Allah ne ya sanya na zama Gwamna ba wani mutum ba.”
“Allah kadai nake tsoro kuma komai karfin mutum b azan ji tsoronsa ba.”
“Na tsaya takara a 2007, da 2011 da 2015 amma duk na sha kasa. Sai ga shi da lokaci ya yi kuma Allah ya sa na zama Gwamna.”
“Kuma ko a yanzu idan mutanen jihar suka yanke shawarar cewa ba sa kaunata zan kama gabana ne na san inda dare ya min,” a cewar Makinde.
A karshe Gwamna ya sha alwashin tallafawa duk wata kyakkyawar manufa da Majalar Yarbawan ta bullo da ita domin ci gaban ’yan kabilar da kuma kasa baki daya.