Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa kuma tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya musanta sha’awar tsayawa takarar shugabancin Najeriya a 2027.
Wannan ya biyo bayan bayyanar wasu hotunan fastar takarar Ganduje tare da Gwamnan Jihar Imo, Hope Uzodinma, a matsayin mataimakinsa.
Waɗannan hotunan sun bayyana ne, jim kaɗan bayan wasu rahotannin na nuni da cewar ana ƙoƙarin cire Ganduje a matsayin shugaban jam’iyyar APC na ƙasa tare da ba shi muƙamin jakada.
Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa (NWC) na jam’iyyar APC, ya ce waɗannan rahotanni game da takarar Ganduje ba su da tushe bare makama.
A wata sanarwa da Sakataren Yaɗa Labaran Ganduje, Edwin Olofu, ya fitar, ya ce waɗannan hotunan an ƙirƙire su ne don haddasa fitina.
Sanarwar ta ƙara da cewa Ganduje yana nan daram a matsayin biyayya ga Shugaba Tinubu kuma yana goyon bayan yadda yake shugabancin ƙasar nan.
Ya yi kira ga jama’a da su yi watsi da waɗannan hotuna na ƙarya kuma kada su yaɗa bayanan da ba su tabbatar da su ba.