✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban yi sanyi ba

Wani Bafulatani ne ya yi laifi, ’yan sanda suka biyo shi da gudu. Yana zuwa wajan wani mai gyaran firji sai ya bude wani firji…

Wani Bafulatani ne ya yi laifi, ’yan sanda suka biyo shi da gudu. Yana zuwa wajan wani mai gyaran firji sai ya bude wani firji ya shiga ciki ya rufe. Ashe dan sandan ya gan shi, yana zuwa sai ya kwankwasa firji ya ce: “Waye a ciki?” Sai danfulani ya ce: “Kunun aya ne da zobo.” dan sanda ya ce: “Fito mu sha.” Sai danfulani ya ce: “Aradu ban yi sanyi ba.”

Daga Muhammad Fagge