✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban yi alƙawarin zama mataimakin kowa a 2027 ba — Obi

Obi ya ce yana da rawar da zai taka duk da ba shi da muƙami a gwamnatance.

Ɗan takarar shugabancin ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya ce ba shi da sha’awar zama mataimakin kowa a zaɓen 2027.

Ya bayyana hakan a shafinsa na X (Twitter) a ranar Asabar.

Obi, ya yi bayanin cewa wasu mutane sun sauya maganganun da ya yi a wata hira da gidan talabijin na News Central TV.

Ya ce ya yi cikakken bayani a hirar, amma wasu sun juya maganarsa zuwa wani abu daban.

“Don kaucewa shakku, ban taɓa faɗin cewa zan zama mataimakin kowa ba. Wannan ba gaskiya ba ne,” in ji Obi.

Ya ƙara da cewa yana maraba da haɗin gwiwa da waɗanda ke da niyyar gina sabuwar Najeriya, amma bai mayar da hankali ga zaɓen 2027 ba, saboda halin da ’yan Najeriya ke ciki na yunwa, talauci, da rashin tsaro.

Obi ya ƙara da cewa lokacin da aka tambaye shi game da haɗin kai, ya bayyana cewa yana maraba da haɗin kai idan tsarin waɗanda ke son a yi ya yi daidai da nasa kan inganta Najeriya.

Ya nanata cewa yana tare da jam’iyyar Labour Party, kuma idan wani yana son yin aiki tare da shi, dole ne su bayyana ainihin manufarsu.

“Ba ni da son zuciya wajen zama shugaban ƙasa ko neman wata kujera. Na yi imani zan iya taimaka wa Najeriya ta hanyoyi da dama, kamar yadda na riga na fara yi, ba tare da riƙe wani ofishi ba,” in ji shi.

 

Obi ya ƙara da cewa idan ya yanke shawarar tsayawa takara a 2027, ba zai yi tafiya da waɗanda burinsu kawai shi ne samun damar iko ba.

Maimakon haka, ya ce yana son shugabannin da za su mayar da hankali kan magance matsalolin ƙasar na, kamar dawo sanya yaran da ba sa zuwa makaranta da kuma rage talauci.

“Kalamaina a zahiri suke, kuma na yi mamakin yadda aka sauya su. Ina da ƙwarin gwiwar taimakon Najeriya, kuma na yi imani zan iya yin tasiri ko ba tare da riƙe wani ofishi ba,” in ji Obi.