✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Ban yarda ana daukar cuta daga wanzamai ba’

Wani mai sana’ar wanzanci a Legas mai suna Malam Alhasan Wanzam, mai kimanin shekaru 45, ya soki lamirin wadanda suke alakanta sana’ar wanzanci da cututtuka.Alhasan…

Wani mai sana’ar wanzanci a Legas mai suna Malam Alhasan Wanzam, mai kimanin shekaru 45, ya soki lamirin wadanda suke alakanta sana’ar wanzanci da cututtuka.
Alhasan Wanzam, wanda ya gaji sana’ar wanzanci, iyaye da kakanni, a kauyen Sakwaya da ke garin Dutse a Jihar Jigawa, ya bayyana wa Aminiya cewa sana’ar wanzanci lafiya take sama wa jama’a. “Ita sana’ar wanzanci, magani ce ga dan Adam. Ba yadda za a yi mutum ya dauki cuta daga wurinmu, sai dai ya sami lafiya. Ko da maganar cutar kanjamau da ake yi a yanzu, ba a daukarta daga wurinmu. Da ma in dai kai ma’abocin neman mata ne, to kana tare da cutar kanjamau, amma ba daga wurinmu ba, saboda mu  kafin mu yi aiki, sai mun tsaftace kayan aikinmu, haka zalika idan muka gama, muna sa ruwan zafi da magunguna mu wanke kayan aikinmu”.
Ya ci gaba da cewa, “Ka ga kamar aski ne idan aka yi wa mutum sai ka ga ya sami lafiya. Haka zalika kaho, shi ma idan wani jini ya tsaya wa mutum ko kuma aka yi wa mutum allura, maganin ya ki tafiya, idan aka yi wa mutum kaho aka tsaga sai ka ga mutum ya sami lafiya”.
Malam Alhasan, wanda ya ce tun yana karami ya fara sana’ar wanzanci ya bayyana cewa bai sha wahala sosai ba wajen koyon sana’ar saboda gatan da yake da shi.
Ya bayyana cewa ban da aski da kaho da cire beli yakan ba da magungunan gargajiya ga jama’a. “Ka san ita sana’ar wanzanci tana da sirri da yawa. Shi ya sa ita sana’a ce da take bukatar biyayya. Idan kana biyayya, babu shakka za ka sami ilimi mai yawa”. Inji shi.
Ya kara da cewa yakan yi amfani da aska da koshiya da reza da kofi da sabulu da mudubi da man shafawa da kuma man sifirit, cikin kayayyakin da yake gudanar da sana’ar tasa.