✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban san ministocina ba kafin in nada su- Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce bai san ministocinsa ba kafin ya nada su. Shugaban ya bayyana cewa ya yi amfani da bayanan tarihinsu ne kawai…

Shugaba Muhammadu Buhari ya ce bai san ministocinsa ba kafin ya nada su.

Shugaban ya bayyana cewa ya yi amfani da bayanan tarihinsu ne kawai ya nada su.

Mai taimakawa Shugaba Buhari kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ne ya sanar da hakan a wajen taron liyafar da aka shirya wa Shugaba Buhari a birnin Abakaliki, wanda Gwamnatin Jihar Ebonyi ta shirya.

Shugaba Buhari ya ce “wasu daga cikin wadanda suke rike da manyan mukamai a gwamnatina , kamar ministoci, za su fada muku cewa ban san su ba a da kafin in nada su.

“Kawai na ga sunayensu ne, sai na yi amfani da tarihinsu da na samu, kuma ina alfaharin cewa ina da mai’aikata masu nagarta da aminci,” inji shi.

Buhari ya nanata cewa yana lura da abin da zai fi kyau ga ‘yan Najeriya ne a kowace shawara da zai yanke.

Hakanan kuma Shugaba Buhari ya yaba wa mutanen Jihar Ebonyi bisa yadda suka amince da kokarinsa na gyara kasa. Sannan kuma ya bukaci ‘yan Najeriya su ci gaba da addu’o’in Allah Ya sa mutanen da za su ci gaba da jagorancin kasar nan su zama masu tsoron Allah.