✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ban ji dadin sanya hotona a labarin rikicin Kannywood ba – Rahama Sadau

Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Rahama Sadau, ta koka kan yadda aka sanya hotonta a labarin da aka wallafa kan yadda batun biyan…

Fitacciyar jaruma a masana’antar fina-finai ta Kannywood, Rahama Sadau, ta koka kan yadda aka sanya hotonta a labarin da aka wallafa kan yadda batun biyan ‘yan fim wanda ya raba kan masana’antar.

Jarumar dai ta nuna rashin jin dadin yadda a ka  sa hotonta a labarin da aka wallafa a kan batun yadda biyan’ yan fim ya raba kan Kannywood, wanda ya samo asali tun bayan hirar da shashen ya yi da Ladin Chima, daya daga cikin jaruman na Kannywood .

Jarumar ta bayyana hakan a ne a kafar sadarwa ta Twitter inda ta bayyana cewa ita ba tace komai ba a cikin wannan rikici amma kuma BBChausa sun sanya hotonta a cikin jerin wadanda rikicin ya shafa.

Jarumar dai ta sake wallafa labarin a Twitter tare da rubuta”To ni kuma mai ya kawo hotona ciki?, neman magana ko me?” a jikin labarin.

Wannan ya sa mutane dake bibiyar shafin tofa albarkacin bakinsu a kai, inda wasu ke ganin kafar BBC ta yi amfani da hoton nata ne domin jan hankalin masu karatu.

Sai dai kuma a cikin labarin, BBC ta bayyana yadda jarumar da ma wasu daban irin su Adam Zango suka nuna nuna alamar yin shiru, duk da sun nuna akwai magana.