✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ban ga dalilin barazanar tsagerun Neja Delta ba — Buhari

Tsagerun Neja Delta sun yi barazanar ci gaba da fasa bututun mai.

Shugaba Muhammadu Buhari ya mayar wa da kungiyar tsagerun Neja Delta martani kan barazanar da ta yi na ci gaba da kai hare-hare a kan harkokin man fetur a yankin.

Cikin wata sanarwa da ta fitar tun a karshen mako, kungiyar ta zargi Gwamnatin Tarayya da gazawa wajen biya mata bukun da ta gabatar mata.

A kan haka ne kungiyar ta kaddamar da wani shiri wanda ta yi wa lakabi da ‘Operation Humble’ kuma ta sha alwashin fara kai hare a kan bututun man fetur da ma wasu ’yan siyasa a yankin na Neja Delta.

Sai dai a yayin da yake mayar da martani, mai magana da yawun shugaba kasa, Mista Femi Adesina, ya ce, gwamnati ta riga da daukar duk wani mataki na biya wa yankin bukatun da aka gabatar mata.

“Rahotanni da dama sun karade kafafen yada labarai cewa kungiyar tsagerun Neja Delta wacce aka fi sani da Niger Delta Avengers, ta ayyana cewa za ta fara kai hare-hare kan muhimman tashohin man fetur muddin ba a biya mata bukatunta ba.

“Kuma abin mamakin shi ne yadda wannan barazana ke zuwa kasa da sa’a 48 bayan da Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin yankin da kuma shugabannin kabilar ijawa a fadarsa, inda suka tattauna batutuwan da suka shafi koken al’ummar yankinsu,” a cewar Adesina.

Ana iya tuna cewa, a Jumaar da ta gabata ce Shugaba Buhari ya gana da shugabannin Neja Delta da na Ijaw a fadarsa ta Villa da ke birnin Abuja.