Tsohon Sanatan da ya wakilci Kaduna ta tsakiya a Majalisar Dattijai, Shehu Sani, ya nemi Gwamnatin Tarayya ta ba ’yan Najeriya hakuri bisa rufe bodar kasa da ta yi.
Shehu Sani ya ce rufe iyakokin tsandaurin ba wani amfani da ya kawo sai ma lalata tattalin arzikin Najeriya, da kuma jefa ’yan kasar cikin halin ha’ula’i.
- Rarara da mawakan 13×13 sun yi waka kan matsalar tsaro
- Maleriya: Mutum milyan 2.8 Suka je asibiti a Kano a 2021
Ya ce: “Ba mu cim ma komai ba da rufe iyakokinmu, sai dora wa mutane talauci. Rufe iyakar Najeriya bai hana ’yan bindiga da ’yan ta’adda shigo da makamai su ci karensu ba babbaka ba.
“A bangaren shigo da shinkafa da aka hana, shin mun noma wadatacciya? Amsar ita ce a’a.
“Sai ma farashin ta da ya hauhawa fiye da lokacin da iyakoki ke bude,” inji shi.
Ko a safiyar Talata ma dai da yake tofa albarkacin bakinsa kan bude iyakokin, Sanatan ya ce tun da rufe su bai yi amfani ba, kamata ya yi gwamnati ta fito ta ba wa ’yan kasa hakuri.
A farkon makon nan ne dai Gwamnatin Tarayya ta sanar da sake bude iyakoki hudu bayan shafe tsawon shekaru sun garkame.