✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Ban damu da rade-radin korata ba – Wenger

A nasa maratanin, kocin Arsenal da ke Ingila Arsene Wenger ya ce ko kadan bai damu da irin rade-radin da ake yi a kafofin watsa…

A nasa maratanin, kocin Arsenal da ke Ingila Arsene Wenger ya ce ko kadan bai damu da irin rade-radin da ake yi a kafofin watsa labarai na yiwuwar korarsa daga kulob din a karshen kakar wasa ta bana ba tun  bayan da kulob din Manchester City ya lallasa na Arsenal da ci 3-0 a wasan karshe a Gasar cin kofin Carabao na Ingila a ranar Lahadin da ta gabata.

Wenger ya ce a nasa tsarin horarwar da zarar ya kammala wasa, to hankalinsa kan karkata ne a kan wasa na gaba.  “Da zarar na kammala wasa, to zan fi mayar da hankali ne a kan yadda zan tunkari wasa na gaba”, inji Wenger.

Tun bayan da Man City ta lallasa Arsenal a wasan karshe ne masana harkar kwallo suke ta hasashen kulob din zai iya sallamar Wenger a karshen kakar wasa ta bana.

Yanzu kofin da kulob din Arsenal yake hankoron ganin ya lashe shi ne kofin Europa wanda ya kai matakin zagaye na biyu kuma kulob din zai hadu da na AC Milan na Italiya ne nan da ’yan kwanaki masu zuwa.